Birnin Kano da Najeriya baki ɗaya an shiga ruɗanin jimanin kisan-gillar da wani ɗan Chana ya yi wa budurwar sa mai suna Ummukhulsum Buhari.
Mutumin mai suna Geng Quanrong ya kashe marigayiyar ce wato Ummukhulsum a ranar Juma’a, ta hanyar tsallaka katangar gidan su ya riƙa caccaka mata wuƙa, ya kashe ta.
PREMIUM TIMES ta ji cewa Geng ya kashe masoyiyar ta sa, bayan ta ƙi auren sa, alhali sun kwashe tsawon lokaci su na soyayya.
Ummukhulsum ta ƙi auren sa, sai ta yi aure da wani, amma daga baya ta fito ta na zawarci. A zawarcin kuma sun ci gaba da soyayya, amma kuma ta ƙi auren sa, bayan ta ci kuɗin sa.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kano Abdullahi Kiyawa ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano ya sa an maida wanda ya yi kisan a Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Bompai, inda daga can za a maka shi kotu, bayan kammala bincike.
Wakilin mu ya tabbatar da cewa tun daga ranar Asabar labarin ya bazu ko’ina a Kano da kewaye, inda a kasuwanni, cikin gidaje, makarantu da dukan wuraren da jama’a ke taruwa, labarin kisan da masoyin ya yi wa masoyiyar sa a ke yi.
Ko a cikin motocin haya da Keke NAPEP da shaguna ko kantinan zamani, wato super market, labarin wannan kisa ake ta yi.
Labarin kisan ya mamaye kafafen yaɗa labarai na zamani, soshiyal midiya, musamman Facebook, TikTok, Instagram da Tiwita.
Discussion about this post