Idan muka yi duba da yadda kakar siyasa ta ke kankama da ƙaratowar zaben 2023, kowace gwamnati a irin wannan lokacin ta kan dage ta ga ta warware matsalolin da kan iya kawo mata cikas wajen samun nasarar ta.
Ko da yake za a iya cewa da ga cikin manyan matsalolin da mulkin Buhari ya fuskanta shine gazawar shawo kan matsaloli masu girma kamar na su ASUU, kai hatta rigingimun jamaiyar su ta APC ya samu irin wannan kalubale, har sai da rigimar ta dau tsawon shekaru, wanda da kyar suka iya yin congress da zabar shugabanni.
Ko da yake yanzu dai lokaci ne wanda ‘duk mai kaza a aljihu ba garejen cewa asss’ lokaci ne wanda a ke tunanin jamaiyya mai mulki zata dauki darasi a kan abin da yafaru da yar uwatta a 2014 da yadda ta kasan ce a 2015.
Ba karamin gaganci bane wasa da rashin bada muhimmaci a alamarin da ya shafi ilimi.
Ko da a nazari na siyasa, in a ka yi la’akari da muhinmancin bangaren ilimi da kuma tasirin sa a siyasan ce duba da yawan miliyoyin mutanen dake cikin alamarin jami’a kai tsaye, a kwai ayar tambaya yadda jami’an wanan gwamnati ke yiwa wannan matsalarar rikon sakainar kashi.
Ko da yake matsalar ma’aikatan jami’a da gwamnati ba sabuwar matsala ba ce, kusan gwamnato cin da suka gabata sun fuskaci irin wannn matsalar, amma irin salon da gwamnatin Buhari ta dauka a irn wannan lokaci da ta ke fuskantar zabe, a kwai hatsari ga nasarar APC.
A kwai abin nazari da tamabaya yadda wannan gwamnati ta kasa kawo karshen wannan matsalar duk da cewa ta sha daukan alwashin kawo karshen matsalar.
Manyan mutanen kasa kamar su sarkin Musulmi Sulatan Abubakar da shugaban ICAN tun a watan February, kwanaki kadan kafin a dunguma wannan yajin aikin, sun ziyarci Shugaba Buhari don shiga tsakani, wanda ya tabbatar musu zai kawo karshen matsalar, sai gashi ya gagara, amma abun mamaki a yanzu shine suma sunyi shiru.
Hatta shugabannin Majalissar kasa, suma sun shiga tsakani a baya, kuma suma sun tabbabatar da kawo karshen wannan matsala. Shin me yasa suma suka yi shiru har zuwa daukan wannan mataki.
Shima dan takara Shugaban Kasa na APC Bola Tunubu yace zai shiga tsakani don kawo karshen wannan matsala, kobme yasa yayi jinkiri?
Jami’an gwamantin Buhari basa son nasarar APC a 2023.
A wannan lokaci da ya kamata a ce wannan gwamnati kanta a hade yake wajen warware duk abin da zai iya kawo mata cikas a 2023, sai gashi akasin haka ne ke faruwa.
Rashin fahimta da fada a tsakanin manyan ministocin buhari a kan wannan rigima, zai iya zama ayar tambaya.
A lokacin da Ministan Kwadago Chriss Ngige ke tsaka da yin sasanto da wadannan kungiyoyi, sai gashi ance ya cire hannun sa a ciki, shi kuma Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya ce zai sasanta a cikin mako biyu, tunda ga lokacin ba a sake jin bakin Ngige ba a kan matsalar, sai kawai jin sa a kayi ya tafi kotu domin sasanto da ASUU da sauran Kungiyo yi Ma’aikatan Jami’a ya gagara.
Wannan karara ya nuna rashin hadin kai da aiki tare tsakanin jami’an gwamnatin Buhari.
Zuwa kutu da FGN karara yana nuna gazawar Ministan Ilimi na yin aikin da yace zai iyayi a kasa da makonni uku.
Tabbas inda jami’an wannan gwamanti suna son jama’iyar su ta APC ta samu nasara a siyasance da basu yadda sun gaza shawo kan wannan matsalar ba.
Wannan gwamnati ta samu damar sanya baki manyan mutane don kawo sasanto, kamar yadda na fada a baya.
Amma jami’an wannan gwamnati sun yi watsi da wannan damar.
Ba abin mamaki bane in har wannan in har wannan matsala ta faru, domin wadannan ministoci na Buhari basa takara, kuma wasu a cikin su sun sami tangarda ne da iyayen jama’iyar.
A siyasa irin ta Nijeriya yiwa Jama’iya zagon kasa ko kauda kai wajen kawar da matsalar da zai iya kawo cikas, ba wani abune sabo ba.
Amma dai akwai daure kai a irin wannan lokaci FGN ta shiga kotu da su ASUU duba da yadda shari’ar kan iya daukan salo iri-iri da kallo iri-iri, wannan tamkar bawa abokan hamayya ne damar yin tasiri a zukakan yan kasa musamman ma wayanda wannan yajin aiki ya shafa.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post