Kwanaki uku bayan wasu jami’an ‘yan sandan kwansitabulare sun yi zanga-zangar hana su alawus-alawus na tsawon watanni 18, yanzu kuma Shugaban Hukumar ICPC ya tabbatar da cewa hukumar sa ta fara binciken salwantar maƙudan kuɗaɗe a Hukumar Gidauniyar Inganta Aikin ‘Yan Sanda, Police Trust Fund (PTF).
Shugaban ICPC, Bolaji Owasonage ya yi wannan tabbacin a wani taron da aka gudanar da Hedikwatar ICPC, ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce akwai tabbacin zargin amfani da ofis a ɗibga badaƙala, karkatar da kuɗaɗe ta hanyar ƙirƙiro dalilai na ƙarya, kwasar kuɗaɗe ana bayarwa ba gaira ba dalili da sauran haramtattun hanyoyin karkatar da kuɗaɗe.
An dai kafa Gidauniyar PTF cikin 2019 domin tara kuɗaɗen inganta aikin ‘yan sanda, ta yadda za su riƙa gogayya da na sauran manyan ƙasashe wajen ƙwarewa da sanin aiki. Sai dai kuma hukumar tun bayan kafa ta, ta fi maida hankali wajen rinto, aringizo da gidogar karkatar da kuɗaɗen ‘yan sandan Najeriya.
A wurin taron wanda Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya halarta, akwai kuma Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola da Babban Hafsan Tsaron Ƙasa Manjo Janar Lucky Irabor.
Shugaban ICPC ya ce, “ana sace maƙudan kuɗaɗen da ake tarawa domin ganin an inganta ‘yan sandan Najeriya da kuma inganta aikin su domin su riƙa gogayya da na sauran manyan ƙasashe.”
Ya ce wannan satar maƙudan kuɗaɗen tsaro ba a Hukumar PTF kaɗai ta tsaya ba, har da sauran ɓangarorin tsaron ƙasar nan.
“Sauran ɓangarorin tsaro su ma ana fama da wannan matsalar salwantar maƙudan kuɗaɗen inganta tsaro. Kuma ana fama da harƙalla sosai wajen ɗaukar jami’an tsaro aiki a ɓangarorin tsaron ƙasar nan.”
“A yanzu haka ma ana kan binciken wasu tsoffin hafsoshin sojoji da wasu tsoffin shugabannin ɓangarorin tsaro saboda zargin hannun da su ke da shi wajen karkatar da kuɗaɗen inganta tsaro a ƙasar nan.
“Shi ya sa yayin da ake ganin cewa kamata ya yi duk wata barazana ta tsaro, kawai a tura sojoji su murƙushe ta, to yawanci satar kuɗaɗen tsaro da ake yi ne babbar matsalar, shi ya sa ake yawan samun ruruwar matsalar tsaron.” Inji Shugaban ICPC.
Ya ce duk wata nasarar da ake fatan samu domin magance matsalar tsaro, to sai an fama daƙile musabbabin ta, wato karkatar da maƙudan kuɗaɗen ɓangarorin Hukumomin tsaro da ake yi daga sama.
Discussion about this post