Gwamnatin Jihar Anambra ta hana ɗaliban sakandare da na fitamare ɗinka ɗangalallen sket a matsayin kayan makaranta su na zuwa aji da su.
Kwamishinar Harkokin Ilmi ta Jihar Anambra, Ngogozi Chima-Udeh ce ta bayyana haka a ranar Lahadi.
Ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, jajibirin komawar yara makaranta a washegari Litinin.
Ta ce dukkan Sakatarorin Ilmi na makarantun gwamnati da masu zaman kan su, su tabbatar kowace makaranta a faɗin jihar ta kiyaye wannan doka.
Ta ce ba daidai ba ne yara mata su riƙa yin shigar nuna tsiraici cikin makaranta, wurin da ya kamata a ce ɗa’a su ka koya da tsare mutuncin su.
“Tilas rigar makarantar da yarinya za ta saka ya kasance tsawon ta ya kai guiwa ko ƙasa da guiwar. Amma ba za a sake barin kowace ɗaliba ta shiga makaranta sanye da kayan makarantar da tsawon rigar ba ta kasa kai guiwa.” Cewar ta.
Idan ba a manta ba, a kudancin ƙasar nan an sha yin sa-toka-sa-katsi tsakanin Musulmai da Kiristoci kan saka hijabi da mata ɗalibai Musulmi ke yi, lamarin da har sai da ta kai Kotun Ƙoli ta amince kowace ɗaliba za ta iya saka hijabi a Jihar Legas.
Discussion about this post