A yanzu za a iya cewa garin Hadejia dama sauran akasarin yankin jigawa ta gabas ibtala’in ambaliyar ruwan sama yayi sandiyar rayukan mutane da dama sannan kuma anyi asarar gonaki da dunbin dukiya, baya ga dubban mutanen da suka rasa muhallin su.
Ba tun yanzu ba, yankin Hadejia na fama da matsalolin ambaliya wanda ya yi wa mutane da dama ta’adi.
Sai kuma yanzu da damuna ya zo da karfin gaske ya kara tunkuɗa mutane cikin halin ƙakanikayi, juayai da tashin hankali.
Tunda a ka shiga wannan yanayi, babu dare babu rana, Shugaban Karamar Hukumar Hadejia, Bala Umar, a kullun tare yake da mutanen sa, a wurin yin jinga da kula da yan gudun hijira.
Duk da kasancewa dama yana daga ingancin shugaba shiga da damuwa cikin al’amuran mutanen sa, Umar na kan gaba wurin kula da taya mutanen sa jimamin matsalolin da su ka afka.
Sauke nauyin shugabanci shine jajircewa a kan al’amuran al’umma, wajen kare rayuka fa dukiyoyin su, sanan da sadaukar da kai wa wajen kare duk wata masifa da ta tunkaro su iya gwargwadon karfin su gaban.
Ita karamar hukumar Hadejia ita matattarar dukannin mutanen da garuruwan da ruwa ya mamaye, musamman mutanen karamar hukumar Auyo, Kiri Kasamma da Malam Madori.
Yanzu abin da ya ke faruwa duk masu hijira da ruwa ya mamaye garuruwan su suna samun mafaka ne a garin Hadejia, karamar hukuma ta basu masauki.
Duk da cewa mutane da dama suna bada gudunmawar buhuna, kawo kasa da bada abinci ga dubban mutane da suka sadaukar da kansu da yin jinga don ceto mutanen da suka makele a garuruwan da ruwa ya mamaye.
Amma akwai takaici kwarai wata halayya ta zababbun mu wanda wannan hakkin yana kansu, da yan siyasa masu takara.
Maimakon su sadaukar da kansu wajen neman maslaha a kan wannan matsala, sai kawai a ka maida abun kamar wasan kwaikwayo, kawai za su shiga bakin ruwa a tattare wando ko a rike shebur a na daukan su a hoto a na dorawa a shafukan social media.
Tabbas tunanin mutanen Hadejia da kuma bibiyar yadda a ke bin lamarin su a yanzu ya na tasiri a zukatan su.
Amma akasarin wannan kokari da fadi tashi don ganin samun saukin wannan masifa da kusan ta shafi akasarin kauyukan karamar hukumar Auyo, Kiri Kasamma da Malam Madori, wajen basu abinci, magani da tsaro.
Hon. Bala Umar yayi kokari mutuka wajen daidaita husuma tsakanin mutane da suka haɗa da wuraren ake jayayya da juna, bude hanyoyin ruwa da kuma
yin jinga.
Domin kowa ya neman yaya zai kare kansa da ga matsalar ambaliyar ruwa. Bisa tsari na shugabanci da taimakon jami’an tsaro ya sanya a ka samu tsari mai kyau da aiki tare domin samun mafita.
Ya zama dole, al’umar Najeriya da hukumomi su waiwayi yankin Hadejia da mutanen yankin domin kawo musu ɗauki na musamman.
Yana da kyau gwamnatin tarayya da ta jiha da hukumomi masu zaman kansu su taimakawa shugabancin karamar hukumar Hadejia a wannan yanayi da take ciki.
Discussion about this post