Sanata Sankara mai wakiltar Shiyyar Jigawa ta Arewa maso Yamma, ya bayar da tallafin naira miliyan 20, buhunan shinkafa 2,000 da sauran kayan agaji ga waɗanda ibtila’in ambaliya ya yi masu ɓarna a yankin da ya ke wakilta.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Sankara, mai suna Muhammad Nazeephy ya fitar a ranar Talata, kuma ya aika wa wakilin PREMIUM TIMES Hausa, ya ce akwai kuma agajin buhunan yashi ko ƙasa har 1,000 da sanatan wanda shi ne Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a ya bayar.
Agajin dai ya bayar da shi ne ga ƙananan hukumomi 12 kuwa su ne za a raba wa kuɗaɗen da kayayyakin saboda ambaliyar da ta yi masu ɓarnar gidaje da gonaki.
Sankara ya bayar da tallafin a ranar Talata, kuma a ranar ce da kan sa ya yi zagayen gani da ido na irin asarar da al’ummar ta yankin sa su ka yi, sakamakon ambaliyar.
A cikin jimami da alhini, Sankara ya jajanta wa jama’a, tare da yin ta’aziyyar neman rahamar Allah ga waɗanda su ka rasa rayukan su sanadiyyar ambaliyar.
Yayin da ya ke masu jawabi a duk wuraren da ya je yin jajen, Sanata Sankara ya tabbatar masu da cewa ya rubuta wasiƙa kai-tsaye zuwa wurin Ministar Ayyukan Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Umar, domin ta gaggauta kai agajin gaggawa ga al’ummar Shiyyar Jigawa ta Arewa maso Yamma.
“Tun a farkon watan Agusta lokacin da ruwan sama ya fara ƙamari ba ƙaƙƙautawa, na rubuta wasiƙa da hannu na zuwa ga Ministar Ayyukan Agaji da Jinƙai da kuma Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA).
“A cikin wasiƙar na bayyana irin gagarimar barazanar da wannan yanki ke fuskanta daga ambaliya, inda na nemi su gaggauta kawo ɗauki.
“Sannan kuma na sake rubuta masu wata wasiƙar lokacin da ambaliyar ta yi ƙarfi har ta yi mummunar ɓarna.” Inji Sanata Sankara.
Ya ce bayan ya rubuta wasiƙar, Hukumar NEMA ta aika da jami’an ta a dukkan yankunan da ambaliyar ya shafa, inda su ka yi nazarin irin ɓarnar da ambaliyar ta yi da kuma asarar da jama’a su ka tafka.
“Saboda haka ina da yaƙini cewa NEMA za ta kawo agajin gaggawa daga gwamnatin tarayya, sannan kuma ta taimaka wajen sake tsugumar da waɗanda su ka rasa muhallin su ko su ka gudu daga muhallan su.” Cewar Sankara.
Sanatan ya kuma nuna damuwa ganin yadda ambaliyar ta yi ɓarna sosai, ba a dukkan Masarautu uku, wato Gumel, Kazaure da Ringim.
“Ba kuma zan manta ba, a cikin 2019 na gabatar da ƙudirin da na nemi Majalisar Dattawa ta amince da shi, wanda na nemi a duba matsalar yawan ambaliya a ƙasar nan, kuma a magance ta baki ɗaya. Majalisa ta kuma amince da hakan.”
Sai dai kuma Sanata Sankara ya ce canjin yanayi ya sa matsalar ambaliya ta ci gaba da faruwa, inda a yanzu ya ce zai sake tayar da maganar a Majalisa, domin a samu hanyoyin da gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi za su haɗa ƙarfi ya yadda za a magance wannan Matsala, domin a kare rayuka, dukiyoyin jama’a da kuma muhalli baki ɗaya.
Waɗanda za su ci moriyar tallafin sun fito ne daga Ƙananan Hukumomin Ringim, Taura, Babura, Kazaure, Roni, Gumel da Maigatari. Akwai kuma Sule Tankarkar, Gagarawa, Yankwashi, Taura da Garki.
Discussion about this post