Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya yi tattakin musamman tare da jami’an tsaro suka dira titin Kaduna-Abuja da cunkoso ya toshe a sanadiyyar faɗuwar wata babbar mota.
Matafiya da dama sun afka cikin ruɗani da tashin hankali a tsawon kwanakin wannan makon.
Wasu matafiyan sun kwana a hanya ne a dalilin wannan matsala.
Ranar Juma’a, kwamishina Aruwan ya sanar cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta bi diddigin abin domin kawo karshen wannan matsala da matafiya suka faɗa a dalilin wannan cunkoso.
Gari na waye wa kuwa, ranar Asabar kwamishina Aruwan, ‘Agogo sarkin aiki’ ya fantsama tare da jami’an tsaro da ma’aikata suka dira wannan hanya, basu bar wannan wuri ba tun da sanyin safiya, har sai da maraice, sai da suka tabbatar wannan hanya ya buɗe sumul-lumui, matafiya kowa ya kama gaban sa, sannnan suka komo gida.
Aruwan a madadin gwamnatin jihar Kaduna ya mika godiyarsa ga jami’an tsaro da kuma kamfanin Julius Berger, da kuma mutane musamman matafiya bisa gudun mawar da kowannen su ya bada.
Titin Kaduna-Abuja na daga cikin manyan titunan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta lashi takobin ganin an gyara wannan hanya kafin ta sauka daga kujerar mulki.
Sai dai kuma, aikin musamman daga Kaduna zuwa Abuja na tafiyar hawainiya wanda aka dangantashi da hare-haren ƴan ta’adda da suka addabi titin.
A halin da ake ciki yanzu jami’an tsaron Najeriya sun dukufa wajen ganin bayan ƴan bindigan wanda suke samun nasarori da daman gaske.
Discussion about this post