• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Ƴan ta’adda sun gamu da fushin sojojin Najeriya, sojoji sun kashe 50 sun kama 60

    GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

    Yari ya raba tallafin tirela 145 cike maƙil da buhunan masara 145 ga mabuƙata a Zamfara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

Addinin Musulunci Shehu Usman Dan Fodiyo Ya Yada Ba Kabilanci Ba, Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
September 3, 2022
in Ra'ayi
0
Addinin Musulunci Shehu Usman Dan Fodiyo Ya Yada Ba Kabilanci Ba, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Ya ku ‘yan uwana Musulmi, Hausawa da Fulani, da dukkanin mutanen arewacin Najeriya! Kamar yadda kuka sani ne, a ‘yan kwanakin nan wani sharri ya bullo muna, na kokarin raba kan ‘yan uwan juna da suka dade a tare, tare da kokarin haddasa rikicin kabilanci tsakanin kabilun arewacin Najeriya, musamman Fulani da Hausawa.

An samu wasu magabtan mu, makiyan mu suna nan suna ta kulle-kulle, suna ta kulla sharri da makirci, ba dare ba rana, suna ta kai kawo domin su rura wutar gaba da tashin hankali, da zubar da jini tsakanin wannan al’ummah, domin kokarin cimma wata mummunar manufa tasu ta siyasa. Suna son su raba kawunanmu domin su ji dadin mulkar mu. Muyi ta fada da junan mu, muna kisan juna, su kuma suna ta ci gaba.

Don haka ya zama dole kuma wajibi ga dukkanin al’ummar arewacin Najeriya, da mu san cewa ana nan fa ana kokarin shirya muna wani tuggu da sharri, don haka sai mu bude idanun mu, mu lura, mu kara kulawa sosai, mu farka daga bacci, domin mu hada karfi da karfe, mu yaki wadannan miyagun mutane.

Makiya Musulunci da Musulmi, makiya ci gaban arewa, daga cikin Nasara, ‘yan bazata, da wasu miyagun ‘yan siyasa ‘yan kudu, suna nan suna ta tsare-tsaren su, suna ta shimfida makirci da sharri domin su cutar da mu, domin su ga sun rarraba kawunan mu, sun haddasa gaba da adawa da yaki da zubar da jini tsakanin mu, su kunna wutar bala’i da tashin hankali da mummunar hayaniya a arewa, wato arewar ta kara rikicewa, bayan rikici da jarabawar da muka samu kan mu a ciki na Boko Haram da barayin daji da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa!

Allah Ta’ala ya hada zumunci mai karfi tsakanin kabilun arewa daban-daban, musamman Hausawa da Fulani; mun zama kamar hanta da jini, mun zama tsintsiya madaurinki daya, muna auratayya tsakanin mu, muna ta kokarin yaya za’a yi da taimakon Allah, mu wanzar da zaman lafiya a tsakanin mu, amma wannan zaman tare namu yana cusawa wadannan makiya namu takaici da bakin ciki a cikin zukatansu, shi yasa suka sha alwashin sai sun raba mu da karfi da yaji!

To wallahi ya zama wajibi, kuma dole mu tashi tsaye, mu nuna masu cewa basu isa ba. Mu nuna masu babu wanda ya isa ya raba mu, ko ya sanya mu muyi tashin hankali tsakanin mu!

Wadannan mutane suna so su nuna cewa Shehu Usman Dan Fodiyo azzalumi ne, wanda ya yaki Hausawa saboda kabilanci, wai ba addinin Musulunci ya karantar ba, wanda wallahi kowa yasan karya suke yi.

Ya ku ‘yan uwana! Shi dai Shehu Usman Danfodiyo wani hamshakin malamin addinin Musulunci ne, kuma mutum ne mai tsoron Allah, masanin addini, wanda ya sake jadadda addinin Musulunci a cikin karni na goma sha tara a kasar Hausa da kewaye; ya kafa daular Musulunci mai fadi, mai karfi da kuma tasiri. Yayi da’awa ta hanyar wa’azi, karantarwa da kuma rubuce-rubucen littafai da wakoki a cikin harshen Fulatanci, da’awar da ta haifar da samun mabiya masu dimbin yawa daga sassa daban-daban na garuruwa masu yawa a kasar Hausa, wanda kuma ya haifar da gwabza yake-yake tsakaninsa da wasu sarakuna da suka yake shi, har ta kai ga ya kafa Daular Musulunci.

Shi dai wannan bajimi, kuma hamshakin Malamin addinin Musulunci, wato Shehu Usman Dan Fodiyo, an haife shi ne a wani gari da ake kira Maratta, wadda yanzu haka ta ke cikin kasar Nijar. Daga nan mahaifinsa yayi hijira zuwa garin Degel, wadda ita kuma yanzu haka take cikin yankin Gobir. A wannan gari na Degel ya girma, ya kuma yi karatun addinin Musulunci, sannan ya fara kira zuwa ga bin Allah da Manzon sa (SAW). Daga baya yayi hijira zuwa Gudu, har zuwa tarewarsa a garin Sakkwato wanda a nan ya rasu, aka kuma binne shi a cikin dakin da ya rasu a cikin gidansa, wanda kuma daga baya gidan nasa ya rikide ya zama hubbarensa da kuma makabartar binne Sarakunan Musulunci da sauran jama’ar da ke kewaye da wannan anguwa.

An haifi Shehu Usman Dan Fodiyo a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba na shekarar 1754. Shi dai da ne ga wani Malami da ake kira Malam Muhammadu Fodiyo. Sunan mahaifiyarsa kuwa Hawwa’u.

Cikakken sunansa shine Usman Dan Muhammad Dan Saleh. Ana kuma kiransa da Shehu Usman Dan Fodiyo. Wannan kalma ta Shehu kalma ce ta larabci, wadda ke da ma’ana ta tsoho ko dattijo, ana kuma amfani da ita wurin kiran wani babban Malami domin girmamawa. Kalmar Fodiyo kuwa, kalmar Fulatanci ce, wadda ke da ma’ana ta Malami, wanda kuma suna ne da aka rika kiran mahaifin Shehu da shi. Ana kiran mahaifin nasa da wannan suna na Fodiyo ne saboda karantarwa da yake yi. Da aka haife shi sai aka gwama kalmomi guda biyu; daya ta Larabci wato Ibn wadda ke nufin da, da kuma daya ta Fulatanci wato Fodiyo, wadda ake nufi da malam. Kenan idan aka ce Ibn Fodiyo, to ana nufin Dan Malam. Kenan idan aka ce Usman Ibn Fodiyo, ana nufin Usman Dan Malam. Idan kuma aka kara kalmar Shehu wadda ita Balarabiyar kalma ce, to sunan yakan koma Shehu Usman Dan Fodiyo, kuma wannan shine sunan da yafi shahara da shi. Haka nan ma ana kiransa da Shehu Mujaddidi.

Shehu Usman Dan Fodiyo ya tashi a gaban mahaifansa. Ya fara karatunsa na Alkur’ani a hannun mahaifinsa. Ya kuma yi karatuttukansa na Larabci da suka hada da yare da kuma nahawu a hannun wani malami mai suna Abdullahi Dan Ahmad. Sannan yayi karatun littattafai da suka kama daga Ishiriniya da makamantanta a hannun wani malami mai suna Usman Bindo mutumin Kabi.

Ya kuma karanta littafin Mukhtasar a wurin baffansa, kuma Dan uwansa Shehi Bindo, wanda kuma shi wannan malami, ya shahara wurin tsoron Allah, da kawo gyara da kuma umurni da aikata kyawawan aiki da kuma hani da aikata mummunan aiki, da kuma mayar da hankali ga abin da yake gabansa. Wannan malami shine malamin da Shehu yayi koyi da shi wurin halaye nagari da kuma kyawawan ayukka. Ya zauna a wurinsa tsawon shekaru biyu, sannan kuma ya dabi’antu da dabi’un wannan malami ta fuskokin jin tsoron Allah, da kuma umarni da aikata kyakkyawan aiki da kuma hani da barin aikata mummunan aiki.

Daga nan kuma sai Shehu ya tafi zuwa ga Shehi Jibirilu, ya zauna a wurinsa tsawon shekara guda. Yayi karatu a wurinsa. Daga baya suka tafi garin Agadas tare da wannan malami a kan hanyar sa ta tafiya aikin Hajji. Da suka iso Agadas sai Shehi Jibirilu ya mayar da Shehu zuwa ga mahaifinsa kasantuwar bai nemi izinin tafiya da shi aikin Hajjin ba.

Daga nan kuma sai Shehu ya koyi fassarar Al-kur’ani mai girma a hannun dan baffansa, kuma abokin wasansa mai suna Ahmadu dan Muhammadu Aminu. Ya kuma halarci majalisin fassarar Al-kur’ani na Malam Hashim, mutumin Zamfara, ya saurari fassarar Al-kur’ani tun daga farkonsa har zuwa karshe.

Ya kuma yi karatun Hadisi na Sahihul Bukhari dukkaninsa, a hannun baffansa Muhammadu Dan Raji, sannan kuma ya jaza masa dukkan abubuwan da ya ruwaito. Haka Shehu ya jajirce wurin neman ilimi har sai da ya kai matsayin malami abin dogaro.

Ya ku ‘yan uwa! Jihadin da Shehu dai yayi shine gwagwarmaya da yaki domin daukaka addinin Musulunci, wanda kuma aiki ne mai matukar muhimmanci da kuma tarin lada a cikin addinin Musulunci. Wannan Jahadi na Shehu Usman Dan Fodiyo an yi shi ne a matakai guda uku: Kira (da’awa, wa’azi), kaura (Hijira) da kuma gwabza yaki (Jihadi).

Shehu ya fara kira lokacin yana da shekaru 20 da haihuwa, a cikin shekarar 1188 bayan hijira (wato 1774 miladiyya). Yayi wannan kira nasa ne ta hanyar wa’azi, da kuma rubuta wakoki cikin harshen Fulatanci. Shehu yana tsaka da wannan kira sai umarnin kora daga kasar Gobir yazo masa daga Sarkin Gobir Yunfa, abin da ya sabbaba masa yin hijira zuwa ga kungurmin dajin Gudu.

Bayan isar su Gudu, sai suka ci gaba da wannan kira, wanda shi kuma shine ya bude kafar fafata yaki tsakanin rundunar makiya da kuma jama’ar Shehu, masu kira zuwa ga tafarkin Allah. An dauki shekaru ana yake-yake daga wannan gari zuwa wancan, wanda daga karshe, Shehu da jama’arsa suka yi galaba a kan Sarkin Gobir Yunfa da jama’arsa, suka kuma kafa cibiyar Daular Musulunci a Sakkwato, a cikin shekarar 1229 bayan hijira.

Shugabanci da jagorancin Shehu Usman Dan Fodiyo ya fara ne tun daga ranar da jama’arsa suka yi masa mubaya’a bayan hijirarsa zuwa Gudu (a matsayin Amirul Mu’minina ko Sarkin Musulmi ko Sultan), a cikin shekarar 1218 bayan hijira. Ya rike wannan matsayi na jagorancin al’ummar Musulmi har tsawon shekaru goma sha uku da watanni bakwai (1218 – 1231).

Kadan daga cikin litattafan da Shehu ya wallafa a rayuwarsa:

1. Kitabun-Nurul Auliya

2. Umdatul Bayan

3. Kitabul Ulumul Mu’amalat

4. Umdatul Ulama

5. Umdatul Muta’abbidin wal Mutaharrifin

6. Mir’atuddullab

7. Hisnul Afham Min Juyushul Auham

8. Asanidud-dha’if

9. Salasilul Zhbaiyya

10. Umdatul Ibad

11. Kaffud-Dalibina an Tafkiru Awamul Muslimin

12. Umdatud-Da’awatul Ibad Ila Kitabullahi

13. Usulul Wilaya

14. Targibu Ibadillah fi Hifzi Ulumi Dinillah

15. Ruju-ul Sheikhul Sanawiy Anittash’didi Fit-taklid

16. Tayizul Muslimin Minal Kafirin

17. Kitabut-Tasawwuf

18. Talkhisu Kitbul Harisul Muhasibi

19. Kitabu Masa’ilul Ummatul Muhammadiyyah

20. Kitabul Faslil Auwal

21. Kitabu Sukussadikin

22. Ihya’ussunnah wa Ikhmadil Bid’ati

23. Kitabusshafa-ul Galili fi Kulli ma Ashkala minal Kalam

24. Sheikuna Jibiril

25. Masa’ilul Muhimmat

26. Kitabul Jihad

27. Tanbiihul Gafilina

Shehu Usman Dan Fodiyo ya rubuta daruruwan littattafai da suka hada da na addini, harkokin gwamnati da mulki, al’adu da kuma al’amurran da suka shafi yanayin kasa. Ya kuma soki lamirin wasu daga cikin shugabanin addini da Malamai a wancan lokacin, ganin yadda suka yi watsi da koyarawar addinin Musulunci, tare da rungumar bokanci, tsafi da tsibbu, wanda hakan yayi karan tsaye ga dokokin addinin Musulunci.

Yayi tir da irin yadda jagororin wancan lokacin suka rinka tsanantawa mutane, ta wurin sanya masu haraji mai tsanani.

A karni na 17 da 18 da 19 Shehu Usman Dan Fodiyo ya taka muhimiyar rawa wurin bunkasa addinin Musulunci tare da samun nasarar jihadi a Futa Buntu da Futa Toro da Fouta Djallon a tsakanin shekarun 1650 zuwa 1750 wanda ya haifar da jihohi uku na Musulunci.

Shehu Usman Dan Fodiyo ya zama abin kwaikawayo ga sauran masu jaddada jihadi a Afrika, irin su Seku Amadu wanda ya samar da daular Masina da El-Hadj Umar Tall wanda ya samar da daular Toucouler, wanda kuma daga bisani ya auri daya daga cikin jikokin Shehu da kuma Modibbo Adama wanda ya samar da daular Adamawa ta Najeriya.

Garuruwan da karantarwar Shehu ta isa kuwa akwai Kano, da Katsina da Zariya da Borno da Gombe da Adamawa da yankunan Nupawa da Ilorin/Kwara, sai wasu yankuna a Jamhuriyar Niger da Kamaru. Muhammad Bello da Dan uwansa Abdullahin Gwandu sun taimaka masa sosai wurin karantarwa da jaddada jihadi tare da tafiyar da sha’anin mulki. Bayan shekara ta 1811 Shehu yayi ritaya daga harkokin mulki tare da ci gaba da rubuta littatafai.

Tun daga farkon kiran Shehu zuwa tabbatar da garin Sakkwato a matsayin cibiyar Daular Musulunci da Shehun ya kafa, Shehu Usman ya zauna a garuruwa da dama. Musamman lokacin da yake wa’azi, kafin yin hijira, ya zauna a kusan dukkan garuruwan yankunan Gobir, Zamfara da kuma Kabbi. Amma duk da haka, ana kiyaye wadannan garuruwa a matsayin wadanda Shehun ya zauna, wadanda kuma har yau akan samu wasu abubuwa da ke tabbatar da zamansa a gurin. Garuruwan su ne kamar haka:

• Maratta: nan ne asalin garin da aka haifi Shehu.

• Degel: shi ne garin da mahaifan Shehu suka zo da shi yana yaro, suka rene shi a nan har ya girma a garin, ya kuma fara kiransa a garin. Wannan gari shine tushen kiran Shehu.

• Gudu: shine garin da Shehu ya zauna gudun hijira.

Shehu Usman Dan Fodiyo ya rasu a ranar Litinin can karshen dare, daidai lokacin sahur, cikin shekarar 1231 bayan hijira. Ya rasu yana da shekaru sittin da uku (63) a duniya. Ya rasu a garin Sakkwato a gidansa da ke cikin unguwar Sabon Birni, wadda a yanzu ake kira Hubbaren Shehu.

Bayan rasuwar Shehu Usman Dan Fodiyo zuwa yau, an yi Sarakunan Musulunci har guda goma sha tara (19), wadanda ya zama wajibi ga dukkan wani Musulmin kirki na kwarai ya girmama su, ya mutunta su, kuma ya kaunace su. Ba domin komai ba sai domin hidimar su ga addinin Musulunci da Musulmi. Sune kamar haka:

1. Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Dan Shehu Usman Dan Fodio.

2. Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Dan Shehu Usman Dan Fodio.

3. Sarkin Musulmi Aliyu Babba Dan Muhammad Bello.

4. Sarkin Musulmi Ahmadu Atiku Dan Abubakr Atiku.

5. Sarkin Musulmi Aliyu Karami Dan Muhammadu Bello.

6. Sarkin Musulmi Ahmadu Rufa’i Dan Shehu Usman Dan Fodiyo.

7. Sarkin Musulmi Abubakar na II Dan Muhammadu Bello.

8. Sarkin Musulmi Mu’azu Dan Muhammadu Bello.

9. Sarkin Musulmi Umaru Dan Aliyu Dan Aliyu Babba Dan Bello.

10. Sarkin Musulmi Abdurrahman Dan Abubakar Dan Abubakar I Atiku.

11. Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I Dan Ahmadu Atiku.

12. Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru II Dan Aliyu Babba Dan Bello.

13. Sarkin Musulmi Muhammadu Dan Ahmadu Dan Ahmadu Atiku.

14. Sarkin Musulmi Muhammadu Dan Muhammadu Dan Muhammadu dan Ahmadu.

15. Sarkin Musulmi Hasan Dan Mu’azu Ahmadu Dan Mu’azu.

16. Sarkin Musulmi Abubakar Sadiq III Jikan Mu’azu.

17. Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki Jikan-Jikan Shehu Usman Dan Fodiyo.

18. Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido Dan Abubakar Sadiq III.

19. Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III Dan Abubakar Sadiq III.

Daga karshe, kuma a takaice wannan shine bayani game da kira da da’awa da kuma karantarwar Shehu Usman Dan Fodiyo, jagoran Musulunci kuma hamshakin Malamin addinin Musulunci.

Da’awar Musulunci yayi, duniya ta shaida haka. Babu da’awar kabilanci a cikin harkokinsa ko kadan! A cikin almajiransa akwai yaruruka daban-daban. Kuma yayi da’awa ne domin yakar zalunci da kuma tabbatar da adalci. Duk wanda ya zargi Shehu da wani abu wanda ba daidai ba, to mu sani, wannan mutum dan iska ne kuma dan tasha, wanda baya nufin wannan al’ummah da alkhairi.

Don haka, ya ku al’ummar arewacin Najeriya, ina kira a gare mu baki daya, da kar mu taba yarda makiyanmu su jaza muna tsiya da fitina da rigima da hayaniya da tashin hankali!

Ya zama wajibi, dukkanin kabilun arewa dole mu hada kai mu zauna lafiya da junan mu. Mu yaki duk wani mutum da yake son cutar da mu ta kowace hanya, kuma ko shi waye.

Allah yasa mu dace, Allah ya kawo muna zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a arewa, da ma Najeriya baki daya, amin.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a wannan lambar waya kamar haka: 08038289761.

Tags: AbujaDan fodioHausaLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

DUBU TA CIKA: An cafke matan da ta haɗa baki da wasu suka sace mijinta sannan suka karɓi miliyan biyu kuɗin fansa

Next Post

Iyaye na ba su ƙaunar Annabi (SAW) shi ya sa rarranƙwala musu taɓarya suka mutu – Munkaila

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Iyaye na ba su ƙaunar Annabi (SAW) shi ya sa rarranƙwala musu taɓarya suka mutu – Munkaila

Iyaye na ba su ƙaunar Annabi (SAW) shi ya sa rarranƙwala musu taɓarya suka mutu - Munkaila

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ba ni kaɗai ne na fidda sunan Ahmed Lawan ya yi takarar shugaban kasa da Tinubu ba, akwai wasu da ke bayan fage – Adamu
  • Yadda bashin da Chana ta hana Najeriya ya kawo cikas a noman shinkafa, da aikin titin jirgin ƙasan Ibadan zuwa Kano
  • SHEKARU 63 BAYAN SAMUN ‘YANCI: ‘Ban so Najeriya ta afka cikin raɗaɗin ƙuncin da ake fama da shi ba’ – Tinubu
  • SHEKARU 63 BAYAN SAMUN ‘YANCI: ‘Za yi wa masu ƙaramin albashi ƙarin Naira 25,000 tsawon watanni 6 a jere
  • SHEKARU 63 BAYAN SAMUN ‘YANCI: Fassarar Jawabin Shugaba Tinubu:

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.