Ɗaliban makarantun gwamnati na jihar Bauchi sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu ga shirin da gwamnatin jihar ta kirkiro na raba ɗalibai mata da maza a makarantu dabandaban.
Ɗaliban sun bayyana cewa yin haka zai sa su rike dogon tafiya kafin su isa makarantun su idan aka raba su da mata.
Sai dai kuma Kwamishinan ilimin jigar Dr Aliyu Tilde da ya ke wa sarkin Bauchi Suleiman Adamu karin haske akan tsarin ya ce gwamnati ta yi haka ne da kyakkyawar niyya.
” Gwamnati ta yi haka ne da kyakkyawar niyya don karfafa wa mata karatun boko har gaba da aji uku na karamar sakandare.
” Mun lura cewa iyaye da dama sukan cire ƴaƴan su mata daga makaranta a lokacin da suka kammala aji ukun karamar sakandare su ya musu aure. Idan muka raba su da maza, makarantun su da ban na mata daban zai kara musu karfin guiwar cigaba da karatu zuwa su kammala babban sakandare.
Yadda tsarin yake
1- Duk makarantar da take da ajujuwa masu yawa, za a raba su zuwa bangare biyu, bangare ɗaya na mata, bangare ɗaya na maza.
2 – Wasu kuma za a raba wurin zama ne, gefe ɗaya maza, ɗaya mata.
3- Inda kuma akwai aji mai A da B, za a raba mata a A, maza a B.
4 – Sannan kuma idan makarantar a kwai rukunin safe da na rana ne, to za a raba, mata su zo da safe, maza da rana.
5,- Wasu makarantun kuma ɗungurugum ne za a raba su. Maza su koma wasu, abar mata a titin inda suke.
A shawarar canja musu makarantun ne, aka samu matsala. Ɗalibai masu zanga-zangar sun ce makarantun da aka maida su sun yi nisan da sai sun biya kuɗin mota kafin su je makaranta ko kuma su tattaki mai tsawon gaske maimakon kusa da suke da makarantun kafin sabon tsarin da ka yi.
Discussion about this post