Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwa masu daraja, ku sani, lallai abun alfahari ne ga dukkanin ‘yan Najeriya maza da mata, babba da yaro, tsoho da tsohuwa, musulmi da wanda ba musulmi ba, da kowace irin kabila daga cikin kabilun Najeriya, cewa ƙungiyar Fulani zalla ta duniya ta zaɓi ɗan Nigeria, wato shugabanmu, Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi II a matsayin zababen shugaban Tabittal Pulaku international na duniya gaba ɗaya. Abin da wannan yake nunawa kenan shine, daga yanzu dai duk wani bafulatanin dake rayuwa a sassan duniya, to yana ƙarƙashin jagoranchin Khalifah Muhammad Sanusi II. Ko a kwanakin baya, kungiyar ta zaɓi Shugabanta na Najeriya, wato tsohon Gwamnan Bauchi malam Isah Yuguda.
Kuma wannan ba wai yana nufin wani kabilanci bane, a’a, ko kuma cewa shi na fulani ne kawai a’a, kawai abinda ake nufi shine, domin a samu cikakken hadin kai da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa tsakanin Fulani, da duk wani mutum da ba bafullatani ba. Kasancewar irin halin da muka samu kan mu ciki a yau, na tashe-tashen hankula, inda wasu miyagu suke kashe makudan kudade, suna rura wutar kabilanci, suna kokarin hada kabilun Najeriya, musamman ma na arewa fada tsakaninsu, domin cimma wasu munanan manufofi nasu.
Idan ba haka ba, wallahi Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi II na kowane, shi mutum ne wanda bai yarda da maganar kabilanci ba sam. Kuma duk wanda yayi hulda da shi, zai tabbatar da haka, kuma zai bayar da cikakkiyar shaida akan hakan.
Saboda haka, muna taya Khalifah Sarki Muhammad Sanusi II murna, Allah ya bashi ikon yin adalci a mulkin sa, amin.
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. 08038289761.
Discussion about this post