Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa bai fa yiwuwa mulki ya ci gaba da dawwama Arewa, bayan Shugaba Buhari ya kammala wa’adin sa na shekaru takwas.
Akeredolu ya yi wannan tinƙahon ne da bugun ƙirji a wurin walimar da mabiya ɗariƙar Cocin Holy Gost ‘yan Majami’ar The Sword of the Spirit ta 40 a Ɗakin Taro na Jami’ar Ibadan.
Ya yi amfani da wannan dama ya shaida wa ɗaukacin Kiristoci cewa su yi amfani da wannan dama ta tikitin Muslim-Muslim su hana mulki dawwama Arewa bayan saukar Buhari.
Ya ce duk wanda ya zaɓi ɗan Arewa a halin da siyasar kasar nan ke ciki a 2023, to ya yi shuka ne kawai a idon makwarwa.
Ya ce kada Kiristoci su bari a yi farfagandar ƙin zaɓen ‘yan takarar Muslim-Muslim a APC.
Akeredolu ya ce abu mafi muhimmanci dai a gare su shi ne mulki ya koma kudu, kada a yi la’akari da addinin ‘yan takara.
Akeredolu ya daɗe ya na fafutikar cewa lallai sai dai mulki ya koma kudu bayan wa’adin shekaru takwas na Buhari.
Sai dai kuma yayin da Bola Tinubu na jam’iyyar su Akeredolu ke APC, shi kuma Atiku Abubakar na PDP ɗan Arewa ne, kuma Musulmi.
Akeredolu wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu baki ɗaya, ya ce kada ‘yan kudu su yi sake fafutikar su ta neman tabbatar da mulki ya koma kudu ta tafi a banza a zaɓen 2023.
Ya yi roƙon cewa kowa ya jingine batun addini duk mai rajistar zaɓe ya fito ya tabbatar ya zaɓi Bola Tinubu, ɗan Kudu kuma wanda a cewar sa ya fi cancanta.
Discussion about this post