Kungiyar ƴan ƴanga da gwamnati ta amince da sun kashe ‘yan bindiga da dama da suka kawo wa garin Batsari hari a jihar Katsina.
Majiya da dama sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bangan sun yi wa maharan zobe ba su sani ba bayan sun kutsa cikin garin Batsari da karfe 4 na maraice.
Batsari na daga cikin garuruwan jihar Katsina da ‘yan bindiga ke yawan kai wa hari sannan garin na da iyakan ƙasa da Jibia, Safana da dajin Rugu.
Mazaunan Batsari da dama sun mutu wasu kuwa sun zama ‘yan gudun hijira a dalilin hareharen ƴan bindiga.
Wani majiya a kauyen ya ce maharan sun shigo garin akan babura dauke da bindigogi kirar AK-47.
” Sun fi shigowa gari a lokacin da muke sallah su tsorata mutane da harbe harbe, sannan su kama na kamawa su yi awon gaba da su, su kwashi dabbobi yadda suke so.
Wani malamin isamiya a garin ya ce yana hanyarsa na shiga garin ne ya ji karar harbin bindiga daga garin.
“Da na ji karar bindigan sai na ruga a guje na koma gida na kulle kofata. Sai da na ji an ce ‘yan sa kai sun shiga garin sannan na fito.
“Ko da na fito na nufi makarantar sakandaren dake garin inda ‘yan bindigan suka saba zama kafin su kawo wa mutane hari na iske babura da bindigogin maharan da ƴannbanga suka sace.
“Wasu ƴan banga sun tare wasu daga cikin ‘yan bindiga yayin da suke kokarin gudu a Kofar yamma.
Wani cikin ‘yan sa kan ya ce ya irga gawan mutum bakwai na ‘yan bindigan amma yana zaton za su fi haka yawa saboda an bisu har can cikin ƙurgurmin daji sun kashe su.
Ya ce da dama daga cikin maharan sun gudu sun bar babura da bindigogin su.
“Zuwa yanzu akwai bindigogi biyu kiran AK-47 da babura shida a hannun mu sannan idan muka bi sawun maharan za mu Kara samun babura da bindigogin su.
Rahotanni sun ce ƴan bindigan na shirin kawo harin ramuwar gayya garin nan ba da dadewa ba.
Discussion about this post