Gwamnonin Najeriya a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), sun ƙi amincewa Gwamantin Tarayya ta fara cirar dala miliyan 418 daga asusun gwamnatocin jihohi, domin biyan wasu dillalan da ke iƙirarin sun yi gada-gadar da su ka cancanci su ci kuɗaɗen.
A cikin wata wasiƙa da NGF ta aika wa Gwamantin Tarayya ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, gwamnonin sun ce duk wani azarɓaɓin da Gwamnatin Tarayya za ta yi don ta gaggauta fara cirar kuɗin, to haramtacce ne, domin a yanzu haka maganar ta na gaban Kotun Koli. Kuma ita Kotun Ƙoli ɗin ta hana a ciri kuɗaɗen tukunna.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya sa wa wasiƙar ƙin yarda a fara cirar kuɗin hannu.
A cikin wasiƙar, sun gargaɗi Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed cewa duk wani ƙulomboton da za su yi don a fara cirar kuɗin, to su sani karya dokar Kotun Ƙoli ce.
Duk wani ƙoƙarin da Minista Malami ya yi har ya sa Buhari ya da amincewa a fara cirar kuɗaɗen, ya haɗu da biirewa da ƙin amincewa daga Gwamnonin Najeriya.
Gwamnonin sun ce tilas tunda batun ya na gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, to ba su yarda a fara cirar kuɗaɗen ba tare da jiran a ji hukuncin da kotu za ta bayyana ba.
Yunƙurin neman fara cirar kuɗaɗen ya zo ne bayan da wani daga cikin dillalan gada-gada mai suna Riok Nigeria Limited, wanda Gwamnatin Tarayya ta bai wa rubutaccen alƙawarin kuɗin kamasho dala miliyan 142 ya garzaya Kotun Ƙoli, bayan shari’a ta kayar da shi a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Ya maka Ƙungiyar Gwamnonin Kotun Ƙoli, inda a ranar 3 Ga Yuni Kotun Ƙoli can ma ta kori ƙarar da ya shigar.
Gwamnonin Najeriya sun ce haramun ne a fara cirar kuɗaɗen su a biya dillalan gada-gadar, tunda Kotun Ƙoli ta ce NGF ko ALGON ba su da hurumin bayar kwangilar da za a ciri kuɗi daga kuɗin su da ke aljihun gwamnatin tarayya a biya masu iƙirarin sun yi kwangilar.
“Don haka korar ƙarar RIOK NIGERIA Ltd da Kotun Ƙoli ta yi, ta shafi miliyoyin dalolin da sauran ‘yan gada-gadar su uku ke neman a biya su.
Salsalar Daɗaɗɗen Rikicin:
Yadda Kotu Ta Hana Kwasar Dala Miliyan 418 Daga Kuɗaɗen Jihohi A Biya Dillalan Gada-gada:
A ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan gada-gada masu iƙirarin cewa sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi ayyukan adadin kuɗaɗen a shekarun baya.
Dillalan gada-gadar sun ce sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi aikin tuntuɓa ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ƙoƙarin aikin dawo masu da kuɗaɗen da aka riƙa ɗibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.
Babban Mai Shari’a Iyan Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar kuɗaɗen da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.
Gwamnonin 36 sun shigar da ƙarar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, waɗanda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).
A ƙarar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa waɗancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.
Lauyoyin sun ce masu iƙirarin sai an biya su haƙƙin kuɗaɗen har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.
“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi kuɗaɗe a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”
Daga cikin waɗanda gwamnoni 36 su ka kai ƙara, har da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Kuɗaɗen Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.
PREMIUM TIMES Hausa a baya ta sha buga wannan gurungunɗumar rikici.
Labarin baya-bayan nan da ta buga, shi ne wanda ɗaya daga cikin waɗanda ke neman a biya su kuɗaɗen, ya ce: ‘Gidoga Gada-gada Ce, Ba Sata Ba’: Ko kukan jini Gwamnoni 36 za su yi, sai an biya mu la’adar Naira biliyan 172 daga asusun su -Ted Nwoko, uban gada-gada.
Wani uban gada-gada kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, sannan kuma hamshaƙin biloniya, Ted Nwoko, ya rubuta wa Ministan Shari’a Abubakar Malami wasiƙa, mai ɗauke da yin tofin tir ga wasiƙar da Gwamnonin Najeriya 36 su ka aika wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed, inda su ka nemi kada ta biya ‘yan gada-gadar gidoga dala miliyan 418, waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a biya su, ba tare da neman shawarar gwamnonin ba.
Nwoko wanda shi ma lauya ne, ya aika da wasiƙar ta hannun lauyan sa Joe Gadzama, inda ya bayyana wa Antoni Janar Malami cewa wasiƙar gwamnonin cike ta ke da jahilcin yadda aka yi har ‘yan gidogar su ka cancanci a biya su kuɗaɗen a matsayin la’adar ayyukan da su ka yi wa jihohin Najeriya da ƙananan hukumomi 774 a baya.
Ted Nwoko wanda ya ce kuɗaɗen idan an biya, shi ke da dala miliyan 142 a cikin dala 418 da za a biya, ya ƙara da cewa ko kukan jini gwamnonin Najeriya za su yi, sai an ɓamɓarar masa kuɗin sa daga asusun su an biya shi.
Ted dai ya aika wa Malami wasiƙar a ranar 6 Ga Satumba, 2021, tare da nuni da cewa babu wani umarni ko hukunci a kotu wanda ya dakatar a biyan sa haƙƙin sa.
Cikin watan Agusta ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi biris da shawarar gwamnonin Najeriya, ya rattaba hannun amincewa a biya ‘yan gada-gadar su shida dala miliyan 418, kwatankwacin fiye da Naira biliyan 170.
Hannun da Buhari ya rattaba ne ya sa Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta umarci Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa (DMO) cewa ya bai wa ‘yan gada-gadar takardun alƙawarin biyan su basussukan cikin shekaru 10.
Bibiyar Musabbabin Kwatagwangwamar Gwamnoni 36 Da ‘Yan Gada-gada 6:
Gwamnoni 36 sun gargaɗi Ministar Kuɗaɗe kada ta biya ‘yan gidoga’ kuɗaɗen.
Gwamnonin Najeriya 36 sun rubuta wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed Wasiƙa, inda su ka gargaɗe ta cewa kada fa ta sake ta biya dala miliyan 418 ga ‘yan kwangilar da gwamnonin su ka ce ‘yan gidoga na gidi.
Wasiƙar dai sun rubuta ta ne ta hannun lauyan su Femi Falana, wanda ya rubuta mata hatsarin da ke tattare da biyan kuɗaɗen.
Falana ya nemi a madadin gwamnonin cewa Minista Zainab ta janye umarnin da ta ba Ofishin Kula da Basussuka (DMO) cewa ya fara shirin bayar da takardun alƙawarin biyan kuɗaɗen a cikin wasu ƙayyadaddun lokuta ga ‘yan kwangilar.
Gwamnonin sun ce ya kamata Minista Zainab ta fahimci cewa sun shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, kuma Kotun Ƙoli ba ta ce a biya kuɗaɗen ba, domin harƙalla ce da dungu da gidoga kawai.
Kuɗaɗen waɗanda dala miliyan 418 ne, idan aka canja su zuwa dala a farashin gwamnati na dala 1 Naira 410, za su kama naira biliyan 171 kenan.
Discussion about this post