Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta kama ‘yan kungiyar IPOB 8 da ake zargi da hannu a kisan jami’an tsaro hudu a jihar.
Kakakin rundunar Micheal Abattam ya sanar da haka ranar Litini.
Idan ba a manta ba a ranar Juma’ar makon jiya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sanda hudu a ofishin su a Jihar.
Abattam ya ce rundunar ta kamo wadannan mutane bayan kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Barde ya bada umurnin kamo wadanda suka kashe ‘yan sandan.
“Nan da nan dakarun ‘yan sanda fantsama zuwa maɓoyar ‘yan IPOB ɗin sai dai ko da suka hango su sai suka buɗe musu wuta amma ‘yan sandan sun fi karfin kayan aiki, nan take suka kama mutum takwas.
Ya ce ‘yan sandan sun kama Chibuike Obioma mai shekara 18, Chidiebere Achazie mai shekara 22, Onyedikachi Nwadike dan shekara 19, Anayo Onyemere mai shekara 51, Ifeanyi Mboyi mai shekara 26, Chukwudi Onyeausi mai shekara 29, Promise Obodo mai shekara 17 da Ebubechi Ifeobu mai shekara 22.
Abattam ya ce rundunar ta kama wadannan mutane a dajin dake tsakanin kauyukan Agwa Izombe dake karamar hukumar Oguta.
“Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa mutanen da muka kama mazauna kauyukan Izombe da Agwa ne.
Barde ya yi kira ga mutanen jihar da su hada hannu da jami’an tsaro domin gamawa da ‘yan bindiga da suka addabi mutane.
Discussion about this post