Sojoji dake aiki a yankin dazukan da ke jihar Kaduna sun yi nasarar dagargaza wasu gungun ƴan bindiga, sun kwato bindigogi da babura.
Kwamishinan tsaro ln jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana a sanarwa ranar Asabar cewa sojojin Najeriya na kasa da na sama sun yi nasarar kashe wasu ƴan bindiga a Galbi dake karamar hukumar Chikun.
A wannan arangama har ta kogi Kaduna sai da aka ratsa.
Baya ga ƴan bindigan da aka kashe, an kwato babura biyar da manyan bindigogi.
Idan ba a manta ba gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a cikin wannan mako ya rubuta wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ke faɗi masa tsananin matsalar tsaro da jihar ke fama da shi sannan kuma da yadda ƴan ta’adda ke shirin mamaye jihar da kuma kafa gwamnati a jihar.
Discussion about this post