Fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna sheikh Ahmed Gumi tare da wani sanata da baya so a faɗi sunan sa ne suka ruwa suka tsaki don gani an sako Abubakar da matan sa Maryam da ƴaƴan su huɗu da ke tsare hannun ƴan bindiga.
Tukur Mamu wanda shine kakakin sheikh Gumi ya bayyana cewa da Gumi da wani sanata da baya son a faɗi sunansa suka tsananta kai komo wajen ganin an saki waɗannan fasinjoji da suka shafe sama da kwanaki ɗari da wani tsare hannun ƴan bindiga.
Waɗanda suka fito sune: Abubakar Idris Garba da shine mahaifin yara huɗun ake tsare da, matarsa Maryama Abubakar Bobbo, sai kuma babban dansu mai shekara 10 Ibrahim Abubakar Garba, Fatima Abubakar Garba 7, Imran Abubakar Garba 5 sai kuma ƴar karamar Zainab Abubakar Garba da shekarar ta 1 da rabi ne kacal.
Shi Abubakar ɗan tsohon gwamnan jihar Kano ne lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, Janar Idris Garba mai ritaya
Sannan akwai wata dattijiya mai suna Aisha Hassan wanda ƴan ta’addan suka saki saboda tsananin rashin lafiya da take fama da shi.
Mamu ya ce tun bayan kallon bidiyon da aka nuno ƴan ta’addan suna jibgar fasinjojin sheikh Gumi cikin tausayi ya saka baki kuma ya tsananta tattaunawa da ƴan ta’addan da rokon su su wa Allah su saki waɗannan yara da iyayen su.
Discussion about this post