A kotun gargajiya dake Mapo a Ibadan ne wata matar aure ta roki kotu ta raba auren ta na shekara 19 saboda tsananin zaman kunci da take ciki a gidan auren ta.
Tawa Olayiwola ta ce ta gaji da aure da mijin ta Ganiu saboda da cin zarafinta da yake yi a koda yaushe.
Ta ce Ganiu baya kula da ita da ‘ya’yan su uku domin ko kudin cefane baya bata sai an yi watanni idan ma ya ga dama ne zai bata naira 1,000.
Tawa ta ce irin wannan hali na mijinta ne ya kawo matsala a tarbiyyar ƴaƴan su yanzu.
“Idan na yi laifi komai ƙanƙantar sa idan ya fara jibga ta ka ce ya sami jaka ce. Sannan idan na gudu makwabta haka nan zai bi ni har can ya haɗa ma da duk wanda ya shiga gaban sa ya gurza min rashin mutunci.
” Sannan kuma ga satan tsiya, ko ɓera albarka. Daga ya kyallara ido ya gani to sunan abin ‘ Sori’ don ko zai yi wuf da shi ya kauce abinsa saboda tsananin dauke-ɗauke da ya riga ya saba da shi.
Tawa ta roki kotu ta raba auren sannan ta kwato mata kudaden ta da Ganiu ya sace.
Ganiu ya amince kotun ta raba auren saboda acewar sa ita kanta Tawa ɗin mazinaciya ce.
Ya roki kotu ta bashi ikon kula da dansu na fari daga cikin ‘ya’ya uku da suka haifa.
Alkalin kotun S.M. Akintayo ya saurari ma’auratan ya umurce su da su zo da ‘ya’yan a zaman kotu na gaba.
Akintayo ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 30 ga Satumba 2022.
Discussion about this post