Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa a ranar Alhamis ta kona giya da ta kwace a hannun wasu mutane a karamar Hukumar Kazaure.
Shugaban Hisbah a Jigawa, Ibrahim Dahiru Garki, ya bayyana cewa giyar da aka kona shi ne karo na tara cikin nasarar da hukumar tayi cikin kankanin lokaci.
Yace adadin kwalaban giya da aka kona a karamar hukumar sun kai kwalba 5,550 wanda adadin kudinsu ya kai fiye da naira miliyan uku da dubu dari biyu.
Ustaz Dahiru Garki ya baiyana cewa hukumar ta kona giyar ne bayan da ta sami umarnin kuto.
Yace addinin musulumci ya haramta sha da da siyar da giya saboda illarsa ga jikin Dan Adam, saboda haka hukumar ta Hisbah ta himmatu wajen taimakawa Al-ummah wajen tabbatar da magance matsalar shan giya a fadin Jihar Jigawa.
Ya kuma cewa dokokin Jihar Jigawa ta haramta sha da siyar da giya. Zasu tabbatar da cewa dokar tana aiki a duk fadin Jihar.
A nasa bayanin, shugaban karamar Hukumar ta Kazaure, Muhammad Muktar Zannah, ya jinjinawa kukumar ta Hisbah wajen aiki tukuru wajen ganin cewa sun tsabtace karamar hukumar ta Kazaure daga miyagun mutane.
Zannan Kazaure yace dama tuni Gwamna Jihar ta Jigawa, Muhammad Badaru, ya bada umarnin rufe gidajen giya dana mata masu zaman kansu a fadin Jihar. Yace tuni karamar kukumar tana aiki da umarnin na gwamna.
A cewarsa, addinin musulumci yayi umarni da hani da mummunan ayuka da kuma umarni da kyakkyawa. Ya shawarci Alummah da su taya hukumumin tsaro da bayanai kan ayyukan baragurbi, saboda kama mai laifi hakki ne na Alummah baki daya ba hukumumin tsaro kadai ba.
Shugaban na karamar hukuma yayi alkawarin taimakawa hukumar ta Hisbah da Mota domin samun damar aiki cikin amince.
A nasa jawabin, Sarkin Kazaure, Najib Husseini Adamu, ya yabawa hukumar ta Hisbah yayi kuma alkawarin cigaba da bawa hukumar ta Hisbah goyon baya.
Sarkin ya sami wakilcin Umar Tafida wanda shi ne iyan Kazaure
Discussion about this post