Wani bene da ake tsakiyar gini mai hawa uku ya rufta kan mutanen da aka tabbatar su na da yawan gaske a Kano.
Hatsarin ya faru a ranar Talata a kasuwar sayar da wayoyin GSM da ke kan titin Beirut Road da ke tsallaken Kasuwar Kantin Kwari.
Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya ce jami’an su sun ceto mutum bakwai da ran su. Kuma su na samun kulawar magunguna.
Saminu ya ce har yanzu jami’an su na ci gaba da binciken yadda za a iya ceto sauran mutanen da ke ƙarƙashin ginin da aka tabbatar su na da yawa.
Ya ce benen ya rufta lokacin da ake ƙoƙarin ƙara masa wani benen a saman ukun.
Lamarin ya faru daidai lokacin da birnin Kano ke tsakiyar fama da ambaliyar da ta shafi unguwanni da dama a cikin birnin.
Discussion about this post