Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Isah Musa mai shekaru 30 wanda ake zargi da aikata laifin yin garkuwa da makwabcin sa kuma abokin mahaifinsa.
Kakakin rundunar Abdullahi Haruna-Kiyawa ya sanar da haka ranar Juma’a a garin Kano.
A ranar 31 ga Yuli da misalin karfe takwas na dare abokin mahaifin Musa ya shigar da kara a ofishin ‘yan sandan dake kauyen Makadi a karamar hukumar Garko a jihar Kano.
“A Karar abokin mahaifin Musa ya ce an kira shi ta wayar salula da ya aika da naira miliyan 100 ko kuma za zo ayi garkuwa da shi ko daya cikin ‘ya’yan sa maza a yi garkuwa da su.
” Ya nemi ayi masa sassauci, a rage yawan kudin domin ya iya biya. Daga nan sai wanda yayi kiran ya ce an rage masa naira miliyan 2.
Kakakin rundunar ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Abubakar Zubairu ya bada umurin a gudanar da bincike domin kamo mutanen da suka kira mahaifin abokin Musa.
“A dalilin binciken da ƴan sanda suka gudanar ya sa suka kama Isah Musa.
“A ofishin ‘yan sandan Musa ya tabbatar cewa mutumin abokin mahaifinsa ne sannan ya hada baki da wani abokinsa domin su yi masa damfara.
Zubairu ya ce rundunar za ta Kai Musa kotu domin yanke masa hukunci da zarar sun kammala bincike.
Ya yi kira ga mutane da su rika kai karar mutane irin haka ofishin ‘yan a mai makon daukan doka a hannun su.
Discussion about this post