‘Yan bindiga sun kashe wani lauya mai suna Benedict Azza a hari da suka kai garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun kashe Azza da karfe 10 na daren Alhamis a Unguwar Saminaka dake makwabtaka da hukumar FRSC.
Shugaban kungiyar Lauyoyin Najeriya reshen jihar Zamfara Junaidu Abubakar ya tabbatar da aukuwar haka ranar Juma’a.
Abubakar ya ce maharan sun biyo marigayi Azza zuwa hanyar gidansa domin su yi garkuwa da shi amma da marigayi ya hango su sai ya juya motarsa ya kama hanyar komawa cikin gari.
Ya ce sai dai kafin ya shiga cikin mutane maharan sun buda masa wuta.
“Bayanin da aka samu shine wasu ‘yan bindiga su biyu a babur sun kashe Azza yayi da yake hanyar zuwa gida a Unguwar Saminaka dake bayan hukumar FRSC.
“Makwabta sun ce sun ji karar bindiga da Karar ƙuginn mota. Sun ce ko da suka fito sun ga Azza ya fito daga cikin motarsa ya hau titi sannan ya zauna jini na malala daga jikinsa
Abubakar ya ce da shi da wasu manyan mambobin kungiyar sun zo wurin da abin ya faru ranar Alhamis.
“Mun iske Azza kwance a cikin jininsa babu abin da aka sata a cikin motar ko daga jikinsa da raunin harsashi uku a jikinsa.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa dake fama da hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
Maharan sun shahara a yin garkuwa da mutane, kisa, sace-sacen dabbobi da sauran su.
Discussion about this post