• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ni da kai na zan zaɓi wanda zai gaje ni, goyon bayan ku kawai nake bukata – Buhari ga Gwamnoni

    Duk da ƙalubalen da mu ke fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Buhari

    MATA KU RIKA SAKA JIGIDA: Sirrika 6 da saka jigida ke yi wa mace – Binciken Masana

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    Yadda rundunar sojin sama suka kashe fitaccen dan bindiga, matan sa biyu da kwamandojinsa 8 a Katsina

    A shafe tarihin wadanda suka soke koyar da tarihi a makarantun Najeriya – Wole Soyinka

    Wole Soyinka ya yi tir da bidiyon barkwanci da shegantakar ‘yan ƙungiyar ‘Pyrates Confraternity’ kan Tinubu

    Duk masu son shugabancin Najeriya su fito su nuna fuskokin su, ba sai lokaci yayi a hadamu da tarkace ba – Muhammadu Sanusi II

    Cire ni daga Sarautar Kano ba zai hana ni ci gaba da faɗin gaskiya ba – Sanusi Lamiɗo

    NDLEA

    Jami’an NDLEA sun kama Faston Coci da durum uku cike makil da muggan kwayoyi

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    Ƴan sanda sun kama mutumin da ya saba Yi wa mata fashi bayan ya zuba musu maganin barci a lemu

    Na zaɓi wanda zai yi mini mataimaki, sunan sa na nan a ƴar takarda a gaban aljihuna na cakale – Tinubu

    Lauya ya maka INEC kotu, saboda zargin akwai dungu cikin fam ɗin takarar da Tinubu ya cike

    Ana batakashi tsakanin ‘yan ta’adda da Sojojin Najeriya a Madallah Abuja

    Najeriya ta tsaurara tsaron kurkukun Katsina, Kebbi da Gusau, don hana farmakin ‘yan ta’adda

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

No Result
View All Result

YAƘIN 2023: Yadda Babachir Lawal da Yakubu Dogara ke wa Tinubu yaƙin-sunƙuru saboda takarar ‘Muslim-Muslim’

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
August 1, 2022
in Labarai
0
YAƘIN 2023: Yadda Babachir Lawal da Yakubu Dogara ke wa Tinubu yaƙin-sunƙuru saboda takarar ‘Muslim-Muslim’

Saɓani, rashin jituwa da rikici a kan takarar Muslim-Muslim ta Bola Tinubu da Kashin Shettima a APC, ta ƙara muni da tayar da ruɗani a cikin APC a makon jiya, yayin da wasu manyan jam’iyyar su ka tabbatar cewa sai sun kunyata APC a zaɓen 2023.

Lamarin ya yi tsamarin da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal su ka kira taron Manyan Kiristocin Arewa ‘Yan APC, a ranar Juma’a a Abuja, su ka yi wannan barazana.

Dama kuma Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta yi tofin tsinuwa kan ɗaukar Shettima a matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa na APC, inda ƙungiyar ta ce cin mutunci ne ga ɗaukacin kiristocin Najeriya.

Yi wa lamarin tir ya ƙara ƙamari lokacin da aka yi zargin APC ta ɗauki sojojin hayar fasto-fasto na bogi, su ka shiga taron ƙaddamar da Shettima. A nan ma CAN ta yi tir da lamarin.

Tawayen Dogara Da Babachir Lawal:

Kafin Lawal da Dogara su haɗa ƙarfi wuri ɗaya, Babachir Lawal tuni ya fito ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa da Shettima, domin a cewar sa, an yi wa Kiristocin Arewa rashin adalci. Sai dai kuma Buhari bai yi hakan ba.

Babachir na daga cikin ‘yan kwamitin da su ka bayar da shawarar wanda Tinubu ya kamata ya ɗauka.

Jin haushin ɗaukar Shettima ya sa Babachir ya ƙudiri aniyar tarwatsa ƙudirin APC. “Tuni an ba mu goron gayyata zuwa yaƙi. Har mun isa sansani, mun kafa tantina.” Inji Babachir.

Za Mu Yi Amfani Da Katin Zaɓe Mu Murƙushe Takarar ‘Muslim-Muslim’ A 2023:

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu dogara, sun ƙara fitowa fili sun nuna rashin amincewar kan takarar Bala Tinubu da Kashin Shettima a APC, takarar da ake kira ‘Muslim-Muslim Ticket’, saboda su biyun duk Musulmai ne.

Babachir Lawal ya ce Kiristoci ‘yan APC za su yi amfani da katin zaɓen su domin su koya wa APC hankali, tunda hankalin ta ya gushe a jikin ta.

Babachir ya ce duk zancen banza ne da ake cewa wai cancanta ce ta sa Tinubu ya ɗauki Kashim Shettima ya yi masa takarar mataimaki, ba addini ba.

Lawal ya ce tsarin ‘Muslim-Muslim’ wata daɗaɗɗiyar ajanda ce ta ture Kiristoci daga mulkin ƙasar nan.

Ya buga misali da ɗaukar Kashim Shettima matsayin mataimakin takarar Tinubu, rashin Kiristoci Kwamitocin NWC da NEC na jam’iyyar APC, ya ce duk tuggun ture Kiristoci ne.

“Kada ma a kawo mana wani rainin wayau a ce wai babu ruwan addini idan ana maganar siyasa. Domin abin da ke faruwa a APC daɗaɗɗen shiri ne sai yanzu aka samu damar fito da shi.

Saboda haka ya ce tun da wuri bai kamata APC ta ci gaba da tafiyar ‘Muslim-Muslim Ticket’ ba, saboda ba wani abin alherin da zai kawo, sai dai ƙara rarrabuwar kawuna tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.

Shi ma tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara, ya yi fatali, tir da Allah–wadai da abin da APC ta yi, wanda ya ce babban kuskure ne da rainin wato, a ce duk cikin Kiristocin Arewa babu wanda zai iya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a APC.

“Tinubu ya yi babban kuskure tunda har ya biye wa gungun waɗanda su ka kitsa tuggun raina mana wayau.”

Dogara ya ce Kiristocin APC za su yi amfani da katin zaɓe domin su koya wa APC hankali.

Cikin manyan baƙi har da Sanata Elisha Agbo da Solomon Dalung.

“Wannan rainin hankali da aka yi mana, zai zama tayar da mu ne daga barci aka yi wa mu Kiristocin Najeriya. Ba mu muka fara wannan siyasar addini ba. APC ce da ‘yan takarar ta su ka fara. Don haka kowanen mu ya tashi tsaye ya yi abin da ya dace mu yi.”

Kun Shigo Da Siyasar Nuna Fifiko Da Raba Kawuna A APC -Dogara:

Dogara ya ce takarar ‘Muslim-Muslim’ siyasar nuna fifiko ce aka yi wa Kiristocin Najeriya, kuma an dasa bambanci da rabuwar kawuna kenan.

Bayan taron manyan Kiristoci a Abuja, Dogara da Babachir sun ziyarci Gwamna Samuel Ortom na Benuwai da Nysome Wike na Ribas.

Ya Tasiri Yaƙin Tawayen Da Dogara Da Babachir A APC?:

Duk da dai Shugaban APC Abdullahi Adamu da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje sun ragargaji Babachir da masu sukar Tinubu saboda ya ɗauki Shettima takarar mataimakin sa.

Ganawar Manyan ‘Yan Tawayen APC Da Wike:

Shi ma Wike da ya karɓi baƙuncin Dogara da Babachir, ya na da jiƙaƙƙa mai tsamari tsakanin sa da Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP na zaɓen 2023. Matsalar ta su ta bijiro ne kan fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP, inda ta kai har kwana ɗaya kafin ziyarar Dogara da Babachir, sai da Wike ya buɗe wa Atiku wuta, tare da kiran sa tantagaryar maƙaryaci, a wani raddi da ya mayar wa Atiku ɗin.

Saboda haka idan ma Dogara da Babachir na son kamun-ƙafar haɗa kai da PDP ne, to Wike ba zai kasance ɗan jagoran da zai kai su ga nasara ba

Kwanan baya shi ma Wike ɗin an ce ya karɓi baƙuncin gwamnoni uku na jihohin Yarabawa masu kusanci da Tinubu. Wasu na ganin cewa Tinubu ne ya turo su wajen Wike ɗin. Shin ko kuwa Dogara da Babachir sun gargaɗi Wike kada ya haɗa kai da APC ne?

Su ma su Dogara da Babachir har yau ba mu ji sun gana da Gwamnonin APC ba. Shin ko gwamnonin babu ruwan su da sha’anin na su ne, su biyu ke kiɗan su, kuma su ke yin rawar su ne?

APC na da Gwamnoni Kirista 6 cikin 22 da ta ke da su a ƙasar nan. Simon Lalong na Filato ne kaɗai Gwamna Kirista a APC a Arewa, kuma sunan sa na cikin sunayen da aka bai wa Tinubu domin ya zaɓi ɗan takarar mataimaki a cikin su. An ce an haɗa da sunayen Babachir da na Dogara. Amma sai Tinubu ya ɗauki sunan Shettima, Musulmi kamar sa. Wannan abu ya ɓata wa Kiristoci rai, musumman ma na Arewa.

Har yau ba a ji Lalong ya caccaki ɗaukar Shettima ɗan takarar mataimaki ba. Sai ma ji aka yi shi ne za a naɗa daraktan kamfen ɗin TInubu.

Sauran Gwamnonin APC biyar duk a kudancin Najeriya su ke. Dukkan su kuma su na yin kalamai ne cikin taka-tsantsan, su na cewa a daina gwamutsa siyasa da addini.

Tsinkayen Da Sule Lamiɗo Ya Yi Wa Rikicin APC:

“Idan da a cikin 2007 ne aka haka, ba komai. Amma yanzu ana yaɗa farfagandar addini a cikin siyasa, har ta rigaya ta yi tasiri. Malamai na magana kan siyasa. Kiristoci na magana kan siyasa. Ba suran mai magana da muryar Najeriya.

“Duk abin da Tinubu zai samu a Arewa, ba zai same shi a Kudu ba. Ni dai ban ga wannan lamari zai iya kai Tinubu gaci ba.”

Tags: AbujaBabachirHausaNewsPREMIUM TIMESYakubu Dogara
Previous Post

2023: INEC za ta raba katin zaɓe cikin Oktoba da Nuwanba – Okoye

Next Post

KWANA ƊAYA BAYAN GANAWAR WIKE DA SU DOGARA: Wike ya karɓi baƙuncin Gwamnonin PDP na yanzu da na da can

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Paparoma bai hana ni karɓar mukamin darektan kamfen ɗin Tinubu ba – Lalong
  • Ƴan sanda sun kama wata tsohuwa da ta yi garkuwa da Almajirai uku a Borno
  • Kotu ta yanke wa ɗan shekara 40 hukuncin zaman kurkuku na shekara 16 bisa zargin kokarin aikata fyade
  • Yadda satar ɗanyen mai, fasa bututu da rashin haƙo wadatacce ke hana Najeriya amfanar tsadar fetur a duniya -NESG
  • Duk da ƙalubalen da mu ke fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Buhari

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.