Gwamna Nyesom Wike ne Jihar Ribas ya caccaki gwamnonin PDP kan ƙoƙarin da ya ce sun yi wajen ganin sai sun hana zaɓen Sanata Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya, amma gwamnonin su ka kwashi buhun kunya, ba su yi nasara ba, cikin 2019.
Ya ce ya amince ne kawai a lokacin saboda babu wani dalili da zai sa a lokacin ya taimaki jam’iyyar APC mai mulki, wadda Lawan da Gbajabiamila ke ciki.
Wike ya ɓallo wannan ruwa a ranar Juma’a, lokacin da Femi Gbajabiamila ke buɗe wasu ayyukan raya jiha da Wike ya kammala.
Gbajabiamila ya buɗe sabbin gidajen ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas ne, waɗanda Wike ya gina.
Haka nan Wike ya ce wasu gwamnoni sun ci amanar sa lokacin rikicin wanda za a naɗa Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa.
A lokacin dai PDP ta amince a naɗa Kingsley Chinda, ɗan PDP daga Ribas, wani makusancin Wike, amma amma sai Gbajabiamila ya bayyana sunan Ndudi Elumelu, ɗan PDP daga Jihar Delta, matsayin Shugaban Marasa Rinjaye.
“Ban yi da-na-sanin kasa taimakon jam’iyyar a wancan lokacin ba, kuma har yanzu ma ban yi ba. Saboda aiki na shi ne na hana jam’iyyar ku sukuni ko ta ina. Saboda haka a Gidan Gwamnatin Ribas na Abuja aka shirya tuggun cewa ‘aka a bari a zaɓi Gbajabiamila.’
“Mun shirya haka, amma sai gwamnonin PDP su ka watsa mana ƙasa a ido, su ka goyi bayan ka. Duk kuwa da mun yarda cewa kada Gbajabiamila da Lawan su samu muƙaman da su ke a kai yanzu.
“A matsayin su na jam’iyyya, sai su ka keɓe su ka goyi bayan ka. Dalili kenan ka sa Ndudi Elumelu ya zama Shugaban Marasa rinjaye. Kuma idan ka tuna, har wasiƙa mu ka rubuta maka cewa ba haka mu ka so ba.” Inji Wike.
Wike ya yi wa PDP barkwanci dangane da yunƙurin da wasu ke yi na neman a tsige Shugaba Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro.
Ya ce Sanatocin da ke wannan hauragiya ai ba su ma da kuzarin iya ci gaba da batun.
“Su mutane ba su son gaskiya. Su na cewa wai za su tsige Buhari. Kurin banza da wofi ne kawai su ke yi. Domin ba za su iya ba.
“Bari mu ga marar kunyar da zai iya tashi tsaye a Majalisa ya ce, ‘Honorabul Kakakin Majalisa. Wayon rashin wayau kawai. Abin da ka san ba ka iyawa, to me ya sa za ka fito waje ka na cika baki cewa za ka yi.” Inji Wike.
Da ya ke magana, Gbajabiamila ya ce darasin da y koya daga wurin Wike shi ne, “a siyasa babu abokin dindindin. Kuma babu abokin gabar dindindin. Amma akwai muradi da buƙatun dindindin.”
Tun bayan da aka fara samun takun-saƙa tsakanin Wike da Atiku, aka fara lura da gwamnan na Jihar Ribas ya fara sinsinar takalmin APC.
Discussion about this post