Tsohon Gwamnan Jihar Enugu kuma a yanzu Sanatan PDP na Enugu, Chimaroke Nnamani, ya bayyana cewa shashanci da jahilci ne ke sa wasu kwaikwayon wasu alamomin rashin lafiya da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ke nunawa a cikin jama’a.
Nnamani wanda ya yi gwamna lokaci ɗaya da Tinubu, daga 1999 zuwa 2007, ya ce a tarihin Najeriya ba a taɓa yin gwamnan da ya samar wa jihar sa ci gaba kamar Tinubu ba, lokacin da ya yi gwamnan Legas.
Daga cikin nasarorin da Nnamani ya ce Tinubu ya samar a Legas, har da samar wa jihar ƙarin kuɗin shiga daga naira miliyan 600 duk wata, zuwa naira biliyan 8 duk wata.
Sai dai kuma duk wa haka, Nnamani ya ce babu ruwan sa da wani Tinubu idan zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya zo, saboda Atiku Abubakar na PDP zai zaɓa.
Nnamani ya ce a zamanin da Tinubu ke gwamnan Jihar Legas, Legas ke da kashi dama da 65 bisa 100 na masana’antun da ke Najeriya.
Haka kuma ya ƙara da cewa a lokacin jihar Legas ke tara kashi fiye da 65 bisa 100 na harajin VAT da Najeriya ta ƙaƙaba.
Yayin da manya da ƙananan yara a sassa daban-daban ke ci gaba da yin bidiyon barkwanci kan Tinubu, shi ma Wole Soyinka ya yi tir da bidiyon da ‘yan ƙungiyar ‘Pyrates Confraternity’ su ka fitar mai ɗauke da barkwanci kan Tinubu.
Wole Soyinka ya yi tir da bidiyon barkwanci da shegantakar ‘yan ƙungiyar ‘Pyrates Confraternity’ kan Tinubu.
Wole Soyinka ya nuna rashin jin daɗin yadda wasu mambobin ‘Pyrates Confraternity’ su ka watsa wani bidiyo inda su ke nuna alamun cin fuska ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
An nuno su a cikin jerin gwano su na rera waƙa mai aibata Tinubu, wadda a yanzu haka ta game duniya. Lamarin da Soyinka ya ce yin hakan rashin mutunci ne, kuma abin ƙyama ƙwarai.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Soyinka ya ce a gaskiya hankalin sa ya kaɗu sosai kuma zuciyar sa ta dugunzuma da ya ji wakar.
“Ni na tashi a cikin al’adar da ba a yarda ana maida wani naƙasu ko tawayar mutum abin dariya ba ko a riƙa yi masa shegantaka. Kuma addinin Yarabawa ma ya yi hani da yin irin wannan shegantaka. Duk irin abin da mutum ya same shi, bai dace a riƙa yi masa shegantaka har ya zama abin dariya ko abin aibatawa ba.
“A haka mu ka tashi a cikin wannan tarbiyya ta mutunta ɗan Adam komai irin nakasun da ya ke da shi. Domin babu wanda ya fi ƙarfin samun tawaya.”
A cikin bidiyon, Kungiyar ‘Pyrates Confraternity’ na bikin cikar ƙungiyar shekaru 70 da kafuwa, su na sanye da rigunan su na ƙungiyar asiri mai launin fari da ja, su na rera waƙa kan Tinubu, yayin da hannayen su da ƙafa ke karkarwa, kamar yadda Tinubu ke yi. An nuno Tinubu ɗin hannun sa na rawa, ya na cewa, “wannan ne lokacin da zan zama shugaban ƙasa.”
Waƙar dai shegantaka ce ta Tinubu tun bayan kakkausan kalaman da ya yi a Gidan Gwamnatin Ogun kafin a yi zaɓen fidda gwani.
Tuni dai ake ta yaɗa bidiyo iri daban-daban inda ake kwaikwayon Tinubu cikin barkwanci da shegantaka, musamman a ko’ina cikin faɗin ƙasar nan.
Discussion about this post