Gwamnan jihar Ribas, Nysome Wike ya zargi wasu daga cikin jigajigan PDP na jihar cewa sune ne suka yi kitsa bita da kullin da ya sa bai samu kujerar takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba.
Idan ba a manta ba tun bayan nasarar da Atiku ya yi a zaɓen Fidda gwani na PDP aka fara takun saƙa tsakanin ɓangaren Atiku da na Wike.
Kusancin su ya daɗa lalacewa bayan Atiku ya zaɓi gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa mataimakin sa a takarar, shugaban Kasa dake tafe.
A taron bukin zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan jihar Peter Odilili wanda aka yi a gari Fatakwal, Wike ya ce ” Wasu ƴan majalisar dattawa kuma jigajigan PDP a jigar Ribas sune suka lashi takobin ganin bayana, kuma suka yi ruwa sukai tsaki ban samu kujerar mataimakin Atiku ba saboda su sun faɗi zaɓen fidda gwani.
Waɗannan sanatoci ,George Sekibo da Barry Mpigi sun koma Abuja, suka rika zabga karerayi akai na harda abinda ban yi ba ma su gogamin bakin tukunya a fuska saboda dukkan su sun faɗi zaɓe shine nima suke so suga bayana.
Bayan haka kuma duk da an naɗa kwamiti domin sasanta Atiku da Wike wanda ya kamata ya fara zama yau Litinin, an dage zamar saboda kusan duka mambobin dake ɓangaren Atiku rashi taron siyasa a jihar Adamawa.
Discussion about this post