Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari wasiƙa mai ɗauke da cewa ‘yan bindiga na ci gaba da kama yankunan karkara su na “gwamnatin su”, tare da kafa sansanin dindindin a dajin Abuja mai kusanci da Abuja, babban birnin Tarayya.
El-Rufai ya yi wa Buhari wannan gargaɗin tun a cikin watan Yuli, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ci karo da wasiƙar.
An tabbatar cewa tun a cikin 2012 ‘yan ƙungiyar Ansaru su ka yi kaka-gida a dajin Birnin Gwari, cikin Jihar Kaduna, bayan sun ɓalle daga Boko Haram.
Rahotannin sirrin da wannan jarida ta bankaɗo sun nuna mafi yawan munanan hare-haren da aka riƙa yi a baya wanda Boko Haram su ka riƙa ɗaukar alhakin kaiwa, Ansaru ne suka riƙa kai su kafin su ɓalle daga Boko Haram ɗin su Shekau.
Masu bincike sun shaida wa wannan jaridar cewa a yanzu ana ƙulla ƙawance tsakanin Boko Haram, JAS, ISWAP, Ansaru da kuma ‘yan bindiga.
Aƙalla mutum 1,192 ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su ka kashe a Jihar Kaduna.
A cikin watanni shidan 2022 kuma idan aka haɗa da kisan rikice-rikicen ƙabilanci, an kashe mutum 645, kamar yadda gwamnati ta bayyana.
Cikin wasiƙar da El-Rufai ya yi wa Shugaban Ƙasa a watan Yuli, ya yi dalla-dallar yadda ‘yadda su ka kakkama ƙauyuka su ka kafa gwamnati.
Ya ƙara da cewa kuma sun ƙwace hada-hadar yankunan da su ka kakkama.
Gwamnan Kaduna ya zayyana wa Buhari yadda Boko Haram su ke ta kokarin kafa sansanin dindindin a cikin dajin Kaduna.
“Rahotannin da mu ke samu da kuma wayoyin su da ake ji idan su na tuntuɓar juna, an tabbatar da ƙoƙarin da su ke yi na kafa sansanin dindindin a Kaduna, cikin yankin da ya haɗe da dajin Jihar Neja.” Inji El-Rufai.
Sun Kafa Dokar Haramta Kamfen Ɗin Siyasa A Wata Gunduma:
“Yan ta’adda sun kafa dokar haramta tarukan siyasa da su ka haɗa kamfen, a yanzu daidai lokacin da zaɓen 2023 ke gabatowa. Musanman a ƙauyukan Maidobiya da Kazage.
Ansaru kamar Boko Haram, ba su ƙaunar dimokraɗiyya da duk wata gwamnatin da ba ta Musulunci ba.
A cikin 2021, yunƙurin aikin sharar fagen ƙidayar jama’a a Jihar Neja bai yiwu ba mazaɓu 9 daga cikin mazaɓu 11 da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Birnin Gwari, saboda farmakin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
“‘Yan Ansaru da ke kewayen ƙauyen Kuyello cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari, sun yi bikin auren wasu ‘yan mata biyu mazauna ƙauyen Kuyello.”
“Yan Ansaru masu yawan gaske sun halarci ɗaurin auren. Bayan ɗaura aure ne Ansaru su ka tafi da amaren biyu cikin dajin Kuduru da ke cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari.”
Yadda Ansaru Ke Karɓar Haraji Daga Hannun Talakawan Jihar Kaduna:
“Ansaru sun ci tarar naira miliyan 1 ga wani Mu’azu Ibrahim a ƙauyen Kuyello, saboda ya sayar da filaye ba da sanin masu filayen ba.”
Gwamnan ya ci gaba da cewa su na bin ɗaiɗaikun mutane su na karɓar haraji da tara daga mazauna yankunan.
An tuntuɓi El-Rufai amma ya ce babu abin da zai ce.
Discussion about this post