Boko Haram da ke zaune a yankunan Kaduna da Neja sun fito da ƙaƙƙarfan shirin tarwatsa kayayyakin samar da hasken wutar lantarki a yankunan Jihohin Arewa maso Yamma.
Haka dai Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya rubuta a cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari, a cikin watan Yuli.
Wannan wasiƙa dai ita ce tabbaci na farko da Gwamnati ta yarda akwai Boko Haram danƙare a cikin Jihar Kaduna.
Ya ce ajandar Boko Haram ta ruguza hanyoyin samar da wutar lantarki a Arewa maso Yamma, ajanda ce ta ƙara jefa yankin cikin ƙunci da durƙushewar tattalin arzikin yankin.
An kashe dubban mutane, dubban ɗaruruwa an raba su da gidajen su, an hana su zuwa gona, sannan an lalata ƙauyuka da daman gaske daga hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
El-Rufai ya ce dandazon Boko Haram sun yi kaka-gidan mamaye wasu yankuna a Ƙaramar Hukumar Chikun cikin Jihar Kaduna da Shiroro da Munya, ƙananan hukumomin da ke cikin Jihar Neja. Waɗannan yankuna su ne kuma ke da manyan Hanyoyin Samar da Hasken Lantarki 330kv (R1M da R2M), waɗanda ke kai wuta zuwa Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara. Jihohi bakwai da su ka haɗu su ka yi yankin Arewa maso Yamma.
“Ya kamata a sani cewa haka kawai ba gaira ba dalili layin samar da wuta na R1M ya mutu a ranar 14 Ga Mayu. Amma saboda dandazon ‘yan Boko Haram da ke yankin, aka rasa yadda za a yi a tura masu gyara yankin domin su duba, su gyara.
“Yanzu haka Arewa maso Yamma kakaf ta dogara ne da layin wuta na R2M, wanda dalilin hakan ya sa ƙarfin wutar ya ragu sosai saboda ƙarancin layin wuta. Da zaran wanann layi na R2M ya samu matsala ko da kaɗan ce, to shikenan Arewa maso Yamma za ta sasance cikin duhu durunɗum. Kuma dama hakan Boko Haram ke so, buƙatar su za ta biya kenan.” Inji El-Rufai.
Idan ba a manta ba, tun cikin 2021 Jihar Neja ta sha sanar da Gwamnatin Tarayya cewa akwai Boko Haram a jihar sun yi kaka-gida a yankin.
Dama kuma akwai Ansaru cikin dajin Birnin Gwari, tun cikin 2012, lokacin da su ka ɓalle daga Boko Haram.
Waɗannan Ansaru ne El-Rufai a wasiƙar sa ta baya-, bayan nan ya rubuta wa Buhari cewa sun “kafa gwamnatin su” a jihar Kaduna.
El-Rufai ya ce tun shekarun baya Boko Haram su ka fara kai wa ma’aikatan wutar lantarki hare-hare idan sun je aikin gyaran Layin Wutar Lantarki na Shiroro-Kaduna.
Ya ce a ranar 13 Ga Yuni 2019 an kai wa gungun masu gyaran wuta hari a Kusasu, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro, bayan sun je aiki a ƙarshen layin wutar. A harin sun kashe ‘yan sanda har uku.
Sun kai wa wasu ma’aikatan hare-hare a Karamar Hukumar Chikun,a ranakun 5 Ga Disamba, 2020 da 16 Ga Agusta, 2021.
“Waɗannan hare-hare ba ƙaƙƙautawa da ake kaiwa kan masu gyaran lantarki ya nuna gagarimin shirin da Boko Haram ke yi na jefa Arewa maso Yamma cikin duhu.
Garuruwan da ke kan waɗannan yankuna sun haɗa da Unguwan Kanti, Kwate, Masaka, Damba, Kadi, Shsnupe, Garu, Kabama da Apituko na Jihar Kaduna.
A ɓangaren Jihar Neja kuwa akwai garuruwa kamar Kaure, Maigu, Kusasu, Nakunna da Ibirro da ke cikin Mazaɓar Galadima-Kogo.”
Manyan jami’an gwamnatin jihohin biyu su na nuna damuwa ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ba ya tashi haiƙan wajen ganin ya matsa lamba an shawo kan matsalar tsaro a yankin.
Discussion about this post