Barayi sanye da takunkumin fuska sun shiga har gidan gwamnatin jihar Katsina inda suka shiga har ofishin sakataren kudi na gidan suka sace naira miliyan 31 dake ajiya a ofishin cikin buhu.
Wannan ba shi ne karon farko da barayi suka afka gidan gwamnatin jihar suka sace kudi.
A cikin 2020, wasu barayi irin haka sun taba shiga gidan gwamnatin har cikin ofishin sakataren gwamnatin jihar suka sace naira miliyan 16.
Wannan karon an ce barayin sun shiga gidan gwamnatin jihar ne da dare a lokacin da shi kansa jami’in dake kula da kudi na gidan Salisu Batsari na wurin aiki.
Wani jami’i dake aiki a fadar gwamnatin jihar da baya so a faɗi sunansa ya ce” Na ji an ce wai a bidiyon da aka dauka na sirri, an ga wani mutum sanye da takunkumi ya rufe fuskar sa ruf, ya haura ofishin ta taga.
Ya ce wannan bidiyo na wurin ‘yan sanda suna bincike akai.
Sanin kowa ne cewa gidan gwamnati na daga cikin wuraren da suka fi ko’ina a jiha tsaro amma kuma a jihar Katsina, barawon zogale da silifa a masallaci zai iya kutsawa kai tsaye ya suntumi buhun miliyoyi ya arce salin alin ba tare da an damke shi ba.
Wannan kamar yadda aka fadi a baya ba shine karon farko irin haka ya ke faruwa a gidan gwamnatin katsina ba.
Discussion about this post