• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Yadda Mahara suka kashe mutum 9 suka sace shanu 500 a Sabuwa, jihar Katsina – Honarabul Danjuma

    RASHIN TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 15 a makon jiya a Najeriya

    Ƴan bindiga sun sace mutum 60 a Rini jihar Zamfara

    Yadda ‘Yan bindiga sun kashe malamin makaranta a jihar Nasarawa

    Ahmad Lawan sitting

    INEC ta yi fatali da sunayen Sanata Lawan da na Akpabio, ta ce hauro da su aka yi ta katanga

    HAJJI 2022: Yadda Ƴan bindiga suka kai wa ƴan haramar zuwa aikin Haji a hanyar su ta zuwa Sokoto daga Isa

    Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 16 suka yi garkuwa da mutane da dama a jihar Taraba

    An yi amfani da ƴan daba ne aka kada ni – Bashir Ahmed

    Buhari ya naɗa Bashir Ahmad mai taimaka masa kan harkokin sadarwa na zamani ‘SA Digital Communications’

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Yadda dakarun Najeriya suka kashe Boko Haram 29, suka ceto mutum 52 da suka yi garkuwa da su

    Buhari ya yi ragaraga da Najeriya, ya jefa ‘yan kasa cikin halin ha’ulai ko ta ko ina ba sauki – Kukah

    2023: Takarar ‘Muslim-Muslim’ rashin adalci ne, ƙara rura ƙiyayya da ƙara nesanta haɗin kan ‘yan Najeriya ne -Hassan Kukah

    BA GUDU BA JA DA BAYA: PDP na gudana a jini na, ko na faɗi zaben fidda ɗan takara, ita zan yi – Wike

    KAƊA HANTAR PDP: Wike ya gayyaci Gbajabiamila da Gwamnan Legas buɗe ayyukan taya jiha, bai gayyaci ‘yan PDP ba

    Ni da kai na zan zaɓi wanda zai gaje ni, goyon bayan ku kawai nake bukata – Buhari ga Gwamnoni

    Duk da ƙalubalen da mu ke fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Buhari

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

No Result
View All Result

WANDA YA RABA FAƊA BAI YI KALLO BA: Sakwarar da su Wike su ka kirɓa, su ka cinye don su yi ƙwanjin kokawa da Atiku

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
August 1, 2022
in Manyan Labarai
0
RIKICIN KWANCE WA ATIKU ZANI A KASUWA: Rundunar PDP ɓangaren Wike sun nemi a tsige Ayu, Shugaban Jam’iyya

Bayanan abin da aka tattauna a taron da Gwamna Nyesom Wike ya yi da makusantan sa, kuma jiga-jigan PDP waɗanda yawancin su gwamnonin PDP ne da ke goyon bayan sa sun fito fili.

A ranar Lahadi ce Wike ya karɓi baƙuncin su a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas, a Maitama, Abuja.

Yawancin waɗanda su ka halarci taron duk gwamnonin da su ka goyi bayan sa ne a zaɓen fidda-gwani, wanda Atiku Abubakar ya yi nasara a kan sa, shi kuma ya zo na biyu.

Da ya ke magana bayan kammala taron, Jerry Gana, wanda mamba ne a Kwamitin Amintattun PDP, ya shaida wa manema labarai cewa gungun magoya bayan Wike sun yi taro ne a karon farko tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, domin su yi bitar abin da ya faru da yadda zaɓen ya kasance, sai kuma matsayin da PDP ta ke a yanzu lokacin da zaɓe ke gabatowa.

Gana ya ce sun ɗauki wata matsaya, amma bai faɗi ko guda nawa ba ne, kuma bai ambaci ko da guda ɗaya ba.

“Mun san dai abubuwa za su kasance, to idan sun kasance ɗin, za mu yi wa ‘yan Najeriya bayani. Saboda wannan ne haɗuwar mu ta farko, tun bayan zaɓen fidda-gwanin da PDP ta gudanar.

“Mun fito ƙarara a tsakanin mu, mun yi bitar batutuwan da ke gaban mu. Kuma mu na sanar da ku cewa kan mu a haɗe haɗe ya ke, a matsayin mu na magoya bayan Wike.”

Majiya a cikin waɗanda su ka halarci taron ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an tattauna tsawon lokaci kan sa-toka-sa-katsin da ake yi tsakanin Wike da Atiku Abubakar.

Wike ya ƙi yarda ya zauna da Atiku tun bayan da ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta matsayin mataimakin takarar sa.

A ranar Juma’a ce Wike ya yi wa Atiku raddin cewa maƙaryaci ne. Kuma wannan rikici ne aka ce ya kawo wa Atiku tsaikon kafa kwamitin kamfen na yaƙin neman zaɓen sa.

Majiya ta ce gungun ‘Wikekeniya’ sun nemi lallai sai dai Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka, ta yadda wani daga kudu zai zama shugaban jam’iyya.

Sun ce wannan ɗaya ne daga cikin sharuɗɗan da su ka gindaya kafin su taka rawa a kamfen ɗin Atiku Abubakar kafin zaɓen 2022.

Gungun sun koka kan yadda shugabancin PDP ya koma kacokan a hannun ‘yan Arewa, alhali kuma daga Arewa ne ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito.

Yayin da shugaban PDP Ayu ɗan Jihar Benuwai ne, kuma na hannun damar Atiku, shi kuma Atiku ɗan Jihar Adanawa ne, duk daga Arewa.

Haka nan kuma sun ce Mataimakin Ayu, Umaru Damagun ɗan Arewa ne daga Jihar Yobe. Haka shi ma Shugaban Kwamitin Amintattun PDP, Walid Jibrin ɗan Arewa ne. Sai Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP Aminu Tambuwal na Sokoto shi ma ɗan Arewa ne.

“Shin ta yaya jam’iyyar da ke tafiya falan-ɗaya za ta iya neman ƙuri’un ‘yan kudu?” Haka wata majiya ta bayyana.

Sun kuma zargi Atiku da yin saniyar-ware da sauran jiga-jigan jam’iyya waɗanda ba makusantan sa ba.

Sun zargi cewa har ma makusantan Atiku sun raba manyan muƙaman gwamnati a tsakanin su, tun ma kafin zaɓen 2023 ɗin ya zo, ba a ma kai ga cin narasa ba.

“Ta yaya ɗan takarar da ke haka tun a yanzu za a yi tsammanin zai canja idan ya zama shugaban ƙasa kuma?”

Aƙalla mutum 51 ne su ka halarci taron, ciki har da gwamnoni biyar, tsoffin gwamnonin PDP bakwai.

Akwai Suleiman Nazifi da tsohon Antoni Janar Mohammed Adoke. Sai Hosea Agboola, Phillip Aduda, Zainab Kure, Garba Lado, Sunday Onoh da sauran su.

Akwai kuma Mohammed Abacha da sauran su.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Wike ya karɓi baƙuncin Gwamnonin PDP na yanzu da na da can.

Yayin da rashin jituwa tsakanin Gwamna Nysome Wike na Jihar Ribas ke ƙara haifar da ɓaraka tsakanin sa da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, Gwamnonin PDP sun kai masa ziyara a ranar Lahadi.

Gwamnonin sun kai ziyarar ce kwana ɗaya bayan da manyan ‘yan tawayen APC, Yakubu Dogara da Babachir Lawal sun kai masa ziyara, jim kaɗan bayan dawowar sa daga bulaguro a ƙasar waje.

Gwamnonin da su ka kai wa Wike ziyara, sun je ne tare da wasu tsoffin gwamnonin PDP, inda a ranar Lahadi su ka gana da shi a asirce, a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ke Asokoro, Abuja.

Ba a san dai abin da su ka tattauna ba. Amma kuma tabbas tattaunawar ba ta rasa nasaba da saɓanin da ke ƙara tsanani tsakanin Wike da Atiku Abubakar.

An samu saɓani tsakanin manyan jiga-jigan PDP ɗin biyu, tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, inda Atiku ya yi nasara, shi kuma Wike ya zo na biyu.

Tun bayan kammala zaɓen dai Wike ya yi tsinuwa da Allah–wadai ga wasu manyan jam’iyyar da ya ce sun yi masa butulci, inda ake ganin da Gwamna Aminu Tambuwal ya ke, wanda ya janye kafin zaɓe, ya ce a zaɓi Atiku.

Wike ya kuma ragargaji masu zaɓen ‘yan takara daga Kudu, waɗanda ya ce sun sayar da ‘yancin ‘yan kudu saboda ‘yan kuɗi kaɗan.

Sannan kuma Wike ya ragargaji ɗaukar Gwamna Okowa na Jihar Delta matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku.

Daga baya Wike ya ce Atiku ya yaudare shi, domin bayan kammala zaɓe, ya bi Wike ɗin har gida ya ba shi haƙuri. Kuma ya ce shi zai ɗauka mataiakin takara.

Ɗaukar Okowa ya fusata Wike, inda ya riƙa fesa wa Atiku munanan kalamai, kuma har yau bai taya Okowa murnar zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP ba.

Kwanan nan Atiku ya fito ya ce masu ba shi shawarar wanda zai ɗauka mataimakin takara, ba su ba shi sunan Wike ba. Wannan furuci daga Atiku ya harzuƙa Wike, har ya kira Atiku ƙasurgumin maƙaryaci.

Gwamnonin da su ka ziyarci Wike sun haɗa da: Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Benuwai, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abiya.

Tsoffin gwamnonin sun haɗa da Donald Duke na Cross River, Gabriel Suswan na Benuwai, Olusegun Mimiko na Ondo, Ibrahim Idris na Kogi da Johan Jang na Filato.

Jiga-jigan PDP sun fara ɗar-ɗar da Wike tun bayan da gwamnonin APC uku daga Kudu maso Yamma su ka kai masa ziyara. Sai kuma ziyarar da Yakubu Dogara da Babachir Lawal su ka kai masa a ranar Asabar.

An ruwaito Wike dai na cewa ba zai fita daga PDP ba.

Tags: AbujaAtikuHausaNajeriyaNewsPDPPREMIUM TIMES
Previous Post

‘Ƴan sanda sun damke ‘ƴan bangan da suka kashe wani malami bisa zargin sace jariri a Kano

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ɗora laifin tsadar fetur kan dillalan mai

Next Post
Petrol Scarcity

Gwamnatin Tarayya ta ɗora laifin tsadar fetur kan dillalan mai

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Wasu jigajigan PDP na jihar Ribas suka kitsa tuggun rashin zama na mataimakin Atiku – Wike
  • RASHIN TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 15 a makon jiya a Najeriya
  • Ambaliyar ruwa ya halaka mutum 50 mutane da dama sun rasa matsuguni a Jigawa
  • Yadda ‘Yan bindiga sun kashe malamin makaranta a jihar Nasarawa
  • JARABA KO BALA’I: Yan sanda sun kama wanda ya yi wa ;yar wata 18 fyade a Bauchi

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.