Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya kamata sanatoci da ‘yan majalisar PDP su daina ɓata lokacin su wajen hayaniyar sai sun tsige Shugaban Ƙasa, domin ba abu ne mai yiwuwa ba a yanzu.
Da ya ke bayani a Zauren Tattaunawar PREMIUM TIMES na Tiwita a ranar Laraba, Sani ya ce “maimakon a tsaya ɓata lokacin abin da su ka san ba mai yiwuwa ba ne a wannan lokacin, kamata ya yi PDP ta maida hankali kawai wajen ganin ta kayar da APC a zaɓen 2023, domin shi ne a gaban mu.
“Kowa ya san Tsarin Mulkin 1999 ya kafa sharuɗɗan tsige shugaban ƙasa, waɗanda a yanzu dai ba a iya tabbatar da su. Abu ne mai wahala da kuma ɗaukar tsawon lokaci kafin a tsige shugaban ƙasa a Najeriya.
“Da za a iya tsige shi, to hakan ne zai fi alheri, amma abu ne wanda ba ma zai iya yiwuwa ba a wannan ƙanƙanen lokaci kuma da irin sanatocin da mu ke da su a majalisa.
“Shi kan sa Shugaban PDP Iyorchia Ayu ai ya yi Shugaban Majalisar Dattawa, ya kuma san cewa abu ne mai wahala tsige shugaban ƙasa. Don haka su ma daina ɓata lokacin su.
“A yanzu yadda zaɓe ke matsowa, su kan su sanatoci da ‘yan majalisa ba za su samu sukunin zama ba, nan gaba kaɗan za ka neme su ka rasa, kowa ya tafi gida gaganiyar cin zaɓe.
“Sannan matsawar akwai irin su Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila a Majalisa, zai yi wahala a samu nasarar tsige shugaban ƙasa a yanzu.”
Shehu Sani ya ce kawai PDP ta maida hankali wajen kayar da APC a zaɓen 2023, ta daina ɓata wa kan ta lokaci kan batun tsige shugaban ƙasa.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Soyinka da Falana sun goyi bayan ‘Yan Majalisar da ke so tsige Buhari.
Fitaccen marubuci Wole Soyinka da fitaccen lauyan kare haƙƙin jama’a, Femi Falana, sun bayyana goyon bayan su ga Sanatoci da ‘Yan Majalisar Dattawa masu neman a tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanatoci da Mambobin dai na PDP sun bayar da wa’adin makonni shida ga Shugaba Buhari ya magance matsalar tsaro, ko kuma su fara shirye-shiryen tsige shi.
Tuni dai wannan kira na su ya fara samun goyon bayan sanatoci daga APC, irin su Sanata Elisha Abbo ɗaga Adamawa da kuma Adamu Bulkachuwa daga Bauchi.
Soyinka ya ce baya ga matsalar tsaro, Buhari ya aikata laifin tsigewa, inda ya yi ƙoƙarin sai ya ɗora wanda zai gaje shi kan mulki. Wannan lamari a cewar Soyinka, karya darajar dimokraɗiyya ce ƙarara.
Batun matsalar tsaro kuwa, Soyinka ya ƙara da buga misali da yadda “wani malami ya nemi ‘yan bindiga sun fara aikin tsige Buhari, ta hanyar gaggauta yin garkuwa da shi da Gwamna Nasiru El-Rufai na Kaduna da ma wasu makusantan Buhari.”
Duk da Soyinka bai ambaci sunan malamin ba, amma dai Sheikh Bello Yabo na Sokoto ne ya yi wannan kakkausan lafazin.
Discussion about this post