• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    TSUMAGIYAR KAN HANYA: An umarci ‘yan sandan Abuja su riƙa binciken motar ko wa kuma ko ɗan wa

    Kotu ta daure magidancin da ya guntile hannun abokinsa kan zargin lalata da matarsa

    Jami’an Kwastam sun kama haramtattun kaya na miliyoyin naira a Katsina

    Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kaya na naira biliyan 6.6 a jihar Ogun

    American University of Nigeria Student -Crt- Google

    Malaman jami’o’i na roƙon a biya su albashin wata da watannin da aka riƙe masu

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    Kotu ta yanke wa mahaifin da ya yi shekara 9 yana lalata da ƴa’ƴan sa mata biyu

    TSUMAGIYAR KAN HANYA: An umarci ‘yan sandan Abuja su riƙa binciken motar ko wa kuma ko ɗan wa

    Ƴan sanda sun kama magidancin da ya yi wa matar makwabcinsa fyade

    ABUJA: Kotu ta daure wasu ‘yan mata biyu saboda yawon gulmace-gulmace a unguwa

    Kotu ta tsare matar da aka kama tana madigo da ‘yar shekara 8 a Kaduna

    Mahukunta a Abuja sun kama ƴan iskan gari mutum 400 da motoci 50 da suka karya doka

    Mahukunta a Abuja sun kama ƴan iskan gari mutum 400 da motoci 50 da suka karya doka

    Tinubu ya naɗa tsohon ministan Abuja, Modibbo, Kakanda, Baba-Ahmed mashawarta a ofishin mataimakin shugaban kasa

    Tinubu ya naɗa tsohon ministan Abuja, Modibbo, Kakanda, Baba-Ahmed mashawarta a ofishin mataimakin shugaban kasa

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    ‘Yan sanda sun kama tsohon da ya yi wa ‘yar shekara hudu fyade a Katsina

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

TSEREN 2023: Yadda NNPP za ta lashe zaɓen shugaban ƙasa daga ƙuri’un jihohi 20 – Buba Galadima

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
August 15, 2022
in Manyan Labarai
0
Buba-galadima

Buba-galadima

Dattijo a jam’iyyar NNPP Buba Galadima, ya bayyana cewa tun a bugun farko jam’iyyar NNPP mai kayan marmari za ta lashe zaɓen 2023 daga ƙuri’un jihohin da ya lissafa guda 20. A Tattaunawar Musamman da PREMIUM TIMES HAUSA a Abuja, Galadima ya bayyana wa irin bambancin salon siyasar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya da irin shirin da jam’iyyar ta yi don lashe zaɓe cikin ruwan-sanyi a jihohi daban-daban.

Galadima ya yi maganganu masu zafi kan matsalar tsaro, bambanci da cancantar Rabi’u Kwankwaso bisa sauran ‘yan takara da kuma yadda NNPP za ta kawo ƙarshen rikicin ƙabilanci da na addini a Jihar Filato.

PT HAUSA: Idan ka yi la’akari da matsalar tsaro a yanzu, shin da a ce ka na a cikin gwamnatin nan za ka yi shiru ne, ko kuwa da-na-sani za ka yi?

GALADIMA: To da farko dai bari na ƙara nanatawa, shi kan sa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha faɗa, ni ma na sha faɗin cewa mu da mu ka fara tafiyar siyasa tare da shi mun bi shi ne ba don idan ya yi nasara ya ba mu wani muƙami ba. Mun yi ne don kishin ƙasa, don kishin al’umma, don kishin addini.

Saboda a lokacin da mu ke ta ƙoƙarin ganin ya yi nasara, kowa ya san a halin da ƙasar ke ciki, duk wanda jama’a su ka yi wa kyakkyawan zato na zahiri da baɗini cewa shi ne zai samar da mafita, to ya kamata a rungume shi. Saboda haka mu irin wannan kyakkyawan zato mu ka yi masa. Allah ya sani, ba don biyan wata buƙata ta daban ba.

Kowa ya yi wa Buhari kyakkyawan zato cewa idan ya zama shugaban ƙasa zai magance matsalolin da aka riƙa kuka da su. Kowa ya yi zaton Buharin da aka sani tsohon Janar wanda ya riƙe muƙamai daban-daban na soja har zuwa Manjo Janar, kuma har zuwa Shugaban Mulkin Soja, zai magance matsalolin da ake kuka a kan su. Amma sai ga shi har ma gara wanda bai ma taɓa ganin soja ba da shi. Zai fi shi taɓukawa.

PT HAUSA: Wannan matsala har ta kai ga wasu rahotanni na cewa a yau Lahadi 14 Ga Agusta, limaman sallatantan birnin Katsina kakaf za su yi taron-dangi yi wa ‘yan bindiga alƙunuti. Me za ka ce, ganin yadda lamarin har ya kai ga haka a cikin Katsina ita kan ta?

GALADIMA: Babu abin da zan ce sai dai ni ma na taya waɗannan malamai da limamai addu’a da jimami da damuwar halin da ba Katsina kaɗai ke ciki ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.

Domin ba sau ɗaya ba ya sha cewa wannan matsala ta fi ƙarfin sa. Ta fi ƙarfin gwamnatin sa. To amma ni ban yarda ba. Niyyar magance matsalar ce kawai bai yi ba.

Saboda me? Kai da ka ke da sojoji, ‘yan sanda da sauran ɓangarorin jami’an tsaro waɗanda sun yi rantsuwar yin aikin kare ƙasa. To don me idan ka bayar da umarni aka ƙi bin umarnin ka, ba za ka kori mutum ba?

PT HAUSA: Tun kafin Gwamna Nasir El-Rufai ya rubuta wa Buhari wasiƙar halin da Jihar Kaduna da kuma Arewa maso Gabas ke ciki dangane da Boko Haram da mahara ‘yan bindiga, Gwamnatin Neja ta sha yin wannan ƙoƙarin kafuwar Boko Haram a cikin jihar. To ganin yadda waɗannan jihohi ke maƙautaka da Abuja, me za ka ce dangane da hare-hare uku da aka kai kusa da Abuja a kwanakin baya?

GALADIMA: To bari na fara tambayar ka. Shi El-Rufai ɗin wane sabon abu ne ya faɗi da har za ku riƙa ganin kamar maganar sa ta sha bamban da wadda sauran ‘yan Najeriya su ka sha faɗa a baya? Me ke ba mu faɗi ba a baya, wanda sabon abu ne da El-Rufai ya faɗi a yanzu?

Na faɗa maka ba wai ya yi wani ƙoƙari a yanzu kafin ya sauka ake magana ba, ko shekara dubu ka ƙara wannan gwamnatin, ba za ta iya iya taɓuka komai ba. Mutumin da ke sa a yi aiki amma babu bibiya, me zai iya yi kuma?

Kafin harin Kurkukun Kuje da na sojoji a Bwari, ai tawagar kwamba ɗin motocin Shugaban Ƙasa aka kai wa hari a Katsina. An ce mutum ɗaya aka kashe, amma kai ma ai ka ga gawarwakin da aka riƙa nunawa lokacin da za a rufe su. Allah ya rufa asiri, ya taƙaita ma ba ya cikin kwamba ɗin motocin.

Ina tabbatar maka da waɗannan ‘yan bindiga na da ƙungiya, idan su ka yi kukan-kura har Abuja za su iya shigowa, su kama wanda su ke so su kama.

Saboda haka ni ina ba Shugaban Ƙasa shawara, bayan ya kammala mulkin sa kada ya zauna Najeriya. Ya roƙi shugaban da zai hau bayan sa ya samar masa gidan zama shi da iyalan sa can a wata ƙasa, ya tafi ya yi zaman sa.

PT HAUSA: Ka na cewa gyara ya fita ƙasar ya yi zaman sa.

GALADIMA: Saboda ƙiyayyar sa. Ka ga dai idan ya gama Daura ba ta zaunuwa gare shi. Zai je Kaduna ya zauna ne? Masu ƙiyayya na iya yi masa cune.

PT HAUSA: Jonathan ma a lokacin sa an yi kashe-kashe. Amma ga shi nan ya yi zaman sa abin sa.

GALADIMA: To Janathan bai gyara garin su ba? Ka je ka gani?

PT Hausa: Bari mu tsunduma cikin siyasa haka nan, inda wasu jam’iyyu su ka daka wasoson Sanata da mamba na Majalisar Tarayya masu wakiltar Shugaba Buhari. An wayi gari a yau ba shi da wakilci daga jam’iyyar sa a majalisun ƙasa biyu, duk sun fice daga jam’iyya.

GALADIMA: To ai idan mutane su na tare da kai, su na yi maka biyayya, sai su ka rabu da kai, sai ka binciki kan ka. Yanzu ka duba ka gani a Daura ɗin can kan iyaka, kowa ya san ‘yar sana’ar rufin asirin da jama’a ke yi ta shigo da abinci daga Jamhuriyar Nijar ya hana. Ina Nijar ina Damagaram ina Maraɗi? A da ba duk ɗaya mu ke ba? Mun manta da irin taimakon da Nijar ta yi wa Najeriya lokacin yaƙin Basasa?

Amma ka san giyar mulki kan sa mutum ya yi abin da zai yi da-na-sani daga baya. Ya manta da ‘yan’uwan sa da ke can ne?

Buhari ya nemi gafara da sulhu ga waɗanda ya ɓata wa. Irin su Sule Yahaya Yamma.

PT Hausa: Da irin su Buba Galadima?

GALADIMA: A’a banda ni. Ni na more, na yi magana na faɗi duk abin da ke zuciya ta. Amma dai a ce a ce mutum kamar ABM Muktar Mohammed ya rasu, bai je jana’iza ba. Mahmud Tukur ya rasu, Buhari bai je jana’iza ba. Ibrahim Baban Kowa ya rasu, bai je jana’iza ba. ‘Architect’ Waziri ya rasu, Buhari bai je jana’iza ba. Ai ko na don Allah ba, ko don mutane, ko don bakin mutane, ko don siyasa ya dace ya je.

Babban ɗa na Aliyu ya rasu. Amma har yau ɗin nan ko kira na a waya bai yi ba ya yi min ta’aziyya.

PT Hausa: Masu karatu za su so jin shekara nawa kenan da rasuwar babban ɗan na ka?

GALADIMA: Shekara huɗu da rabi kenan. Har yau ko waya bai yi min ba. Da ya kira ba na kusa, da na gani ko na sani.

Amma aka wayi gari wai waɗanda su ka nemi ganin bayan mu, su ka nemi halaka mu lokacin da mu ke adawa da su, su ne ya runguma.

PT Hausa: Irin su wa kenan?

GALADIMA: Irin su Abdullahi Adamu, irin su Godswill Akpabio, irin su Rotimi Amaechi. Har ma ya nemi su gaje shi.

Sai bayan ya sauka zai yi mamakin satar mutanen sa su ka yi a zamanin mulkin sa. Duk sace-sacen da aka yi, dukiyar da aka yi da lambobin akawun da dalolin da aka canja duk mun tattara mu na da rekod. Bayan ya sauka idan ya riƙa jin abin da aka yi zamanin mulkin sa, to Allah ya sauƙaƙe masa bugun-zuciya.

PT HAUSA: Lokacin kamfen na 2019 ka na tare da Atiku Abubakar. An yi mamakin irin ɗimbin jama’ar da ta tarbi Atiku a zuwan sa Kano. Kowa ya yi tsammanin PDP ce za ta ja mafi yawan ƙuri’u. Amma sai lamari ya sha bamban. Wai me ya sa taron Kano bai yi wa Atiku tasiri a zaɓen 2019 ɗin ba?

GALADIMA: Zan iya rantse maka da Alƙur’ani Atiku ya ci zaɓen 2019, murɗe masa aka yi. Ka tuna kafin zaɓe an tambayi Buhari cewa ‘idan ka faɗi za ka iya taya wanda ya yi nasara murna? Me ya ce? Cewa ya yi shi ba zai faɗi zaɓe ba. Me ya ke nufi?

PT HAUSA: Bayan zaɓe kuma sai ka bar PDP da Atiku.

GALADIMA: Ni fa ban taɓa yin PDP ba. Idan ka tuna a lokacin ni ne Shugaban r-APC. Sai aka yi yarjejeniyar maja da PDP. Mun kuma yi hakan ne saboda yaƙinin mu a lokacin cewa duk wanda ya hau, zai fi Buhari taɓukawa. Saboda haka da Atiku ya karɓi gwamnati a lokacin, ba za a lalace haka ba.

PT HAUSA: Shigar Kwankwaso NNPP ya ruguza PDP a Kano, kuma ya rikita gayyar APC a jihar. To a ƙasa kuma ka na ganin har zai iya fin Buhari da Atiku idan ya hau mulki? Me za ka ce tunda ka yi aiki da Buharin da Atikun?

GALADIMA: Ai Kwankwaso ya fi su ta wurare da dama. Ya fi su ilmi. Ya yi ambasada, wato jakadancin ƙasa. Su kuma ba su yi ba. Ya yi sanata, ya yi gwamna shekaru takwas. Ya na da digiri na 1 zuwa na 3. Ya fi su basira. Ya fi su ayyuka ya na gwamna. Ya kawo zaman lafiya a jihar Kano lokacin ya na gwamna.

Kwankwaso ya fi su tausayin talakawa. Ya fi su tausayin al’umma baki ɗaya. A tausayi da kula da halin da ‘yan Arewa ke ciki, babu kamar Kwankwaso. Duk inda ‘yan Arewa su ke, idan wani abu ya same su, zai je ya yi jaje, bayar da tallafi, ta’aziyya, lallashi da neman haƙƙin su idan an zalunce su.

Mu na da ‘yan gudun hijira a Nijar, Kamaru, Chadi amma masu hali nawa su ka kai masu ziyara da tallafi? Kwankwaso ne.

Wajen gina al’umma kuma, lokacin da ya na Gwamnan Kano, ya riƙa amfani da kuɗin gwamnati ya na tura ɗaliban jihar jami’o’i daban-daban cikin Najeriya har 13.

Ya yi amfani da kuɗin sa ya kai ɗalibai 370 sun yi digiri na biyu a manyan jami’o’in duniya. Ya dauki nauyin ɗalibai 70 sun yi digirin-digirgir, wato Ph.D.

Yanzu haka ya gina jami’a nan yankin Abuja a Masaka. Ya ɗauki ɗalibai huɗu kyauta daga kowace jiha, biyu maza biyu mata.

Sannan ya gina nagartacciyar firamare kyauta a yankin Karu. Ya gina gidan hedimasta, ya gina ofishin hedimasta da ofishin malamai. Ya jina ajujuwa 12, wato aji 1 zuwa 6 kowane A da B. Kuma garin ƙabilar Gwari ne da Gwamdara. Ka ga shi ba a Kano kaɗai ya ke da tasiri ba. A ko’ina.

PT HAUSA: Jama’a na auna ƙarfin NNPP tun daga Kano….

GALADIMA: Ai ba a Kano kaɗai ba. A kowace jiha mun yi kyakkyawan shiri. Gaba ɗaya fa Kwankwaso ya dama wa APC da PDP hankali da lissafi. Ranar zaɓen za su gane kuren su. Saboda mu ake jin tsoro, ba mu ke jin tsoron su ba. Zuwan Kwankwaso Ilorin da Legas ya tayar masu da hankali. Saboda haka ranar zaɓe bugu ɗaya na farko Kwankwaso zai zama shugaban ƙasa.

Ka duba, a Kano PDP ko ɗan takara ba ta da shi. Sannan Kanawa idan su ka tuna irin wulaƙancin da aka riƙa yi wa Kanawa ana kashe su ana ƙwace masu dukiya, ka na jin za su yarda kuma su zaɓe su? Ai Kwankwaso shi ne zaɓin Kanawa.

PT HAUSA: A 2015 an riƙa yi wa Buhari yarfen ba zai iya mulki ba, saboda tsufa ko rashin lafiya. Yanzu kuma ana yi wa Tinubu yarfen tsufa, tangaɗi, rangaji da karkarwar hannaye. Ko wannan zai yi tasiri a yanzu kuwa?

GALADIMA: Ai ko ba a faɗa maka komai ba, ka san san dai bai wa Tinubu mulki, kamar mutum ya faɗo daga sama ne, ya zarce cikin rijiya. Ka dai ga lokacin da Buhari ya miƙa masa tuta. Ya iya riƙewa? Ka dai ga lokacin da ya ke karanta jawabi a takarda. Ya iya buɗe takardar? Wannan kadsio biyun idan mu ka tsaya, sun isa mai hankali ya yi tunani. Ya za a yi Buhari da ke da shekaru 80 ake cewa amma ya fi ɗan shekaru 69 ƙarfi? Ai sai dai ka nemi wajen 85 ko ma 90, amma 69 ba.

Ya rage ga masu zaɓe. Ko su zaɓi Tinubu a koma ‘yar-gidan-jiya. Ko kuma su zaɓi Kwankwaso domin shi ne gatan talaka, gatan al’umma.

PT HAUSA: Amma ba ka ganin batun takarar ‘Muslim-Muslim’ zai iya yin tasiri kuwa?

GALADIMA: Ka san mutane wasu su na yin karatu, amma ba su da ilmi. Kuma kowa akwai fuskar da ya ke kallon dimokraɗiyya. Daidan wani abincin wani. Duk abin da jam’iyya za ta yi don ta ci zaɓe daidai ne idan bai kauce wa doka ba.

APC na ganin sai ta yi Muslim-Muslim za ta iya cin zaɓe. Mu kuwa NNPP babban limamin Kirista mu ka ɗauka mataimakin takara, mu ka haɗa shi da babban shehin mu Kwankwaso. Kawai dai iya ruwa fidda kai. Allah ya ba mai rabo sa’a.

Ka dubi abin da mu ka yi a Jihar Filato. Su ba su bai wa Musulmi takarar gwamna ko mataimakin gwamna. Ga su kuma Musulmi sun fi kashi 40 bisa 100. Me mu ka yi? Sai mu ka ce masu a’a. Mu ka ɗauki fasto da ba shi da tsatstsauran ra’ayi ɗan takarar gwamna. Ya yi zaman Amurka shekaru 17. Ya na da ƙungiyar (NGO) ta Sulhunta Rigingimun Cikin Al’umma (conflict resolution). Ya san idan ya zalunci wata ƙabila ko addini ko wane mutum, akwai sakamako daga Allah.

Sannan mu ka ɗauko Sheikh Abdullahi Ango. Ka ga su biyun nan idan Fasto ya kawo mana ko da kashi 10 bisa 100 na ƙuri’a, Musulmi ya kawo mana kashi 40 bisa 100. Mun lashe Filato kenan. Za a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a jihar. ‘Yan Arewa maso Gabas da ‘yan Arewa ta Tsakiya za su iya ratsa Filato su shigo Abuja hankalin su kwance.

Haka mu ka yi a Taraba. NNPP ce kaɗai ta tsaida ɗan takarar gwamna Musulmi, Sheik Muhammad Sani Yahaya. Kuma Taraba ke da Musulmi kashi 60 bisa 100. Duk sauran jam’iyyun Kirista ne ɗan takarar su.

Saboda haka mun yi kyakkyawan shirin da NNPP ta fi dukkan jam’iyyun da ka sani a Kano, Katsina, Kwara, Neja, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Kogi, Nasarawa, Filato ma za ta kafa gwamnati.

Za a yi gwagwagwa da mu a Yobe, Barno da Benuwai. Za mu ci Kuros Riba, Akwa Ibom, Oyo. Za mu ka daga a Delta. A Legas za mu yagi kashi 25 bisa 100. Dama kuma su mu ke son samu a Legas, buƙata ta biya kenan.

Tags: AbujaBuba GaladimaHausaKwankwasoNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

El-Rufai ne gogarman ruruta wutan rashin tsaro a jihar Kaduna – Shehu Sani

Next Post

INEC ta yi fatali da sunayen Sanata Lawan da na Akpabio, ta ce hauro da su aka yi ta katanga

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Ahmad Lawan sitting

INEC ta yi fatali da sunayen Sanata Lawan da na Akpabio, ta ce hauro da su aka yi ta katanga

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Kotun Amurka ta amince Jami’ar Jihar Chicago na iya jinkirta sakin bayanan karatun Tinubu
  • JAMI’AR GUSAU: Ba tun yau bane ƴan ta’adda ke yi wa ɗaliban jami’ar ɗauki ɗaiɗai
  • ƘALUBALE GA MATAWALLE DA BADARU: Sace Ɗaliban Jami’ar Gusau da Dawowar Ta’addanci a Arewa Maso Yamma, Daga Ahmed Ilallah
  • Wike ya soke lasisin mallakar filayen wasu jigajigan Najeriya ciki har da Peter Obi
  • Kotu ta daure magidancin da ya guntile hannun abokinsa kan zargin lalata da matarsa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.