An bayyana cewa kafafen yaɗa labaran Najeriya sun buga labarin kashe mutum 564, biyan diyyar naira miliyan 653.7 da kuma yin garkuwa da mutum 3,420 tsakanin watan Yuli, 2021 zuwa Yuni, 2022 wato cikin shekara ɗaya kenan a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ƙungiyar SBM mai bibiyan matsalolin rashin tsaro da sauran al’amurra ce ta bayyana haka, tare da cewa iyar wannan adadi kawai waɗanda jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai su ka tabbatar ne.
Saboda haka adadin zai iya wuce haka nesa ba kusa ba, idan an yi la’akari da rahotannin kisa, hari, garkuwa da biyan fansar da ke faruwa a kullum waɗanda jaridu ba su sani ba, ko ba su buga ba.
SBM ta ce ta tabbatar a wannan shekara ‘yan ta’adda sun nemi a biya su adadin da ya kai naira biliyan 6.531, to amma dai an biya su adadin da ya kai naira milyan 653.7.
“Amma wannan lissafi ba a haɗa da maƙudan kuɗaɗen da aka biya fansar wasu matafiya takwas da aka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna. Saboda an biya kuɗaɗen a cikin watan Yuli 2022 ne ba cikin Yuni 2022 ba.
“Rahotanni a cikin Yuli 2022 sun tabbatar da cewa fasinjoji takwas da ‘yan ta’adda su ka saki, sai da kowanen su aka biya Naira miliyan 100 kowanen su. Sai wani ɗan ƙasar Pakistani da aka biya naira miliyan 200 cur.
Binciken SBM na 2020 ya tabbatar da cewa tsakanin Yuni 21 zuwa Maris 2020, an karɓi kuɗin fansar waɗanda aka yi garkuwa dasu har dala miliyan 18.3.
Binciken ya ci gaba da cewa dala miliyan 11 daga cikin kuɗaɗen duk an biya su ne tsakanin Yuli 2016 zuwa Maris 2020.
Discussion about this post