Har yanzu dai ba a fara kamfen karara ba a faɗin kasar nan sai dai ƴan siyasa da ƴan takara suna siyasar mummuƙe ne, wato siyasar sari ka noƙe.
Kowani ɗan siyasa yana ta faman wanki da guga yana shirya adakar sa dumin shirin daga an hura usur ya fallo da gudu ya shiga filin daga.
A jihar Kaduna akwai babbar ƙalubalen dake gaban ƴan siyasan dake neman kujerar ɗan majalisar wakilai ta tarayya wanda zai wakilci Kaduna ta Arewa.
Ƴan takara uku sune suke kan gaba wajen neman kujerar amma kuma abinda ya dada sa takarar take da muhimmanci a 2023 kuma ƴan Kaduna ke son ganin yadda zata kaya shine ganin ɗan gwamnan jihar Bello El-Rufai ne ɗan takarar kujerar na Jam’iyyar APC.
Mutane na ganin gwamnan jam’iyyar har da karfin tsiya ya tilasta wa Samaila Suleiman wanda shine ke kan wannan kujera ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP saboda yana son jam’iyyar ta tsaida da ɗan sa Bello.
Toh, ko haka ne ko ba haka bane, hasashen jama’ a dai haka ya karaɗe jihar.
Bello El-Rufai
Bello El-Rufai matashi ne amma kuma ba a san shi ba kwatakwata a jihar. Wasu da dama na ganin farin jinin mahaifinsa wato gwamna El-Rufai shine zai yi masa tasiri a wannan takara da ya fito sai kuma tarin dukiya da ake ganin yana da su .
Ɗaya daga cikin mutanen Kaduna ba su san shi ba, ba su taɓa jin koda kalami daya ne daga bakin sa musamman game da mutanen yankin Kaduna ta Arewa ko kuma ace wai yau an ganshi a wani wuri da yake kaddamar da wani abu na taimako a faɗin jihar.
Ko wa katambaya zai ce maka shi bai san Bello ba amma ya san mahaifin Bello. Ga dukkan alamu dai mahaifin sa ne da makarraban mahaifin za su yi masa aikin don samun nasara a zaɓen inda zai fafata da gaggan ƴan siyasa irin su Samaila Suleiman da Shehu ABG.
Sannan kuma wasu na ganin abu ɗaya da ƴan Kaduna za su yi su saka wa El-Rufai bisa irin ayyukan da rangaɗa wa mutanen Kaduna da shi kenan su zaɓi ɗan sa ya zama wakilin su a majalisar Tarayya.
Sama’ila Suleiman
Shiko Sama’ila Suleiman da aka fi sani da farar aniya, ya ce ya wasa wukar sa domin za a yi kare jini biri jini ne da koma waye ya shiga gaban sa a wannan takara da ya fito.
Sama’ila ya fice daga APC ya koma PDP sabo da rashin samun tikitin takara da tayi, da ƙarfin tsiya da karfin arzikin sa kuma ya kada Shehu ABG a zaɓen fidda gwani duk da shine ɗan takara na jam’iyyar a wancan lokacin.
Makonni kaɗan kafin zaɓen fidda gwani Sama’ila ya canja sheka ya tsinduma PDP ya buga takarar fidda gwani da ABG, ya kuma kada shi. Wasu masu yin sharhi akan siyasa sun ce wakilai sun samu kudin gaske a wannan zaɓe inda ƴan takaran su biyu suka rika danƙara musu miliyoyin kuɗi.
Sama’ila dai yayi amfani da ƙarfin arzikin sa ya kada ABG.
Shehu ABG
Shehu ABG bai ji daɗin abinda ya faru ba musamman ganin yadda shugabannin PDP suka juya masa baya bayan hidima da yayi wa jam’iyyar a lokacin da Sama’ila ba shi nan.
Da yawa daga cikin magoya bayan ABG na ganin ba a yi masa adalci ba kuma dalilin haka suka canja sheka daga PDP zuwa NNPP.
Yanzu gaba ɗaya yan takaran suna ta wasa wukaken su suna jiran a fara kamfen zuwa kuma lokacin zaɓe wato Faburairun 2023.
A nawa hangen, Sama’ila ya tono tsuliyan dodo, domin zai zama abin kunya da kuri, da cin fuska da rashin kunya ace wai Sama’ila ya kada El-Rufai, domin idan har hakan ya tabbata, toh ko Bello ba hatta shi kansa gwamna El-Rufai zai zama abin magana.
Wannan shine babban dalilin da ya sa na ke ganin akwai aiki ja a gaban Sama’ila, haka kuma shima Bello da ABG.
Discussion about this post