Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya koka da tsadar man ‘diezel’, wanda ya ce a yanzu haka ya na neman gurgunta sana’ar kiwon kifi a ƙasar nan.
Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a wurin Taron Neman Tsayayyen Farashin Kifi na Masu Kiwon Kofin Kudu maso Yamma, wanda aka yi ranar Talata a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Ya ce, “tsadar man diezel’ da tsadar abincin kifi da kuma tsadar dala na kawo cikas da babbar barazana ga masu kiwon kifi.
Tsohon shugaban ƙasar, wanda shi ma hamshaƙin mai kiwon kifi ne a gonar sa da ke Otta, ya shawarci masu kiwon kifi da cewa matuƙar su na so sana’ar su ta ɗore a wannan mawuyacin hali, to su samu tsayayyen farashin da za su riƙa sayar da kifin su, maimakon su riƙa yin cinikin-awon-igiya.
Ya ce a yanzu lita ɗaya ta man ‘diezel’ ta na naira 800. “Kuma duk kilo ɗaya na kifi ana kashe masa naira 1400 kafin a sayar da shi. To idan ba a sayar da shi naira 1,500 ba, an faɗi warwas kenan.” Inji Obasanjo.
“Duk waɗannan matsaloli su na ta ci gaba da afkuwa ne saboda ba dai-dai ake tafiyar da mulkin ƙasar nan ba.
A na shi jawabin, Shugaban Masu Kiwon Kifi na Ƙasa, Amoo Tunbosun, ya ce aƙalla duk shekara ana cin kifi metrik tan miliyan 3.6 a ƙasar nan. Amma kuma ya nuna takaicin cewa metrik tan miliyan 1.1 kaɗai ake iya samu duk shekara a ƙasar nan. Sauran metrik tan miliyan 2.5 duk daga waje ake shigo mana da su.
Ya ce idan ba a yi da gaske ba, to sana’ar kiwon kifi za ta gagara a ƙasar nan. Daga nan kuma miliyoyin mutane za su rasa aikin yi. Sai a dogara da shigo da shi daga waje.
Wannan koke na su Obasanjo ya zo ne daidai lokacin da ake kukan cewa abincin kaji ya yi tashin gwauron zabon da bai taɓa yi ba.