Yayin da Najeriya ke shirin zaɓen 2023 cikin shekara mai zuwa, hujjoji na ƙara bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar fuskantar matsanancin yanayi biyu: wato baitilmalin da ba ko ranyo a ciki, sai kuma raguwar da tattalin ke yi a kullum.
Jami’an gwamnati da manyan ‘yan kasuwar da ke da masaniyar halin da ake ciki, sun ce ana nuna damuwa sosai a Abuja da Legas, yayin da wani zaɓaɓɓen jami’in gwamnati ya jawo hankalin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele cewa abin da ya rage a asusun Najeriya da ke waje fa bai wuce dala biliyan 15 ba, wato ƙasa sosai da dala biliyan 36 ɗin CBN ɗin ya yi iƙirarin cewa su na cikin asusun.
Yayin da Najeriya ta kashe naira tiriliyan 5.9 wajen shigo da kayayyaki daga waje tsakanin Janairu zuwa Afrilu 2022 kaɗai, dala biliyan 15 kacal ɗin ƙasar ke da shi a yanzu ba su wuce kashewa cikin watanni huɗu ba kenan wajen shigo da kayayyaki.
Masana harkokin tasarifin kuɗaɗen sun ce da a ce komai na tafiya daidai, to raguwar kuɗaɗen ba abin damuwa ba ne. Amma abin fargabar shi ne yadda aka shafe watanni shida cur Najeriya ba ta zuba ko sisi a cikin asusun don kuɗin su ƙaru ba. Wannan kuma ya faru ne saboda matsalar rashin wadatar ɗanyen man da Najeriya ke fitarwa waje ne, da kuma tsayuwar gwanin jakin da kasuwar ta yi.
Sannan kuma ɗaukar lokaci mai tsawo da NNPC ta yi ta kada zuba cinikin ɗanyen mai a CBN, shi ne ya haifar da tsawwala farashin dala a kasuwannin ‘yan canji.
Wata babbar ma’aikaciyar banki wadda ta ce wannan jarida ta rufa mata asiri kada ta ambaci sunan ta, ta ce an daɗe ana ɓoye gaskiyar sauran adadin kuɗaɗen gwamnati a cikin asusun waje, wanda babbar matsala ce sosai a halin yanzu.
Ta ce an yi ƙarin gishiri ne wajen ainihin yawan kuɗaɗen da ke CBN, domin kawai a ɓoye ainihin adadin da su ka rage a asusun waje.
An haƙƙaƙe cewa wannan babban jami’in gwamnati wanda kuma zaɓen sa aka yi, ya sanar wa Shugaba Muhammadu Buhari gaskiyar halin da ake ciki na ramewar tattalin arzikin Najeriya. Sai dai kuma Fadar Shugaban Ƙasa ba ta amsa wa PREMIUM TIMES tambayoyin da ta yi kan wannan mawuyacin halin da ake ciki ba.
Sannan kuma maida NNPC hannun jarin masu kasuwanci da aka ce an yi, ya ƙara dagula matsalolin. Wato tunda NNPC ya kasa zuba kuɗaɗen cinikin ɗanyen mai ko na fetur a asusun CBN, tilas kenan bankin ya tashi ya inda zai samu manyan kuɗaɗen ƙasashen waje.
Abin damuwa a nan shi ne, mafi yawan hanyoyin da CBN zai iya samun kuɗaɗen duk a toshe su ke da majinar murar da ta toshe hancin CBN ɗin, wanda kuma shi da kan sa ya ƙirƙiri tsarin da ya haifar da toshewar ƙofofin hancin na sa.
Ma’ana dai tunda asusun ajiyar kuɗaɗe na waje an kasa saka masa komai tsawon watanni huɗu, to ƙasar nan ba ta da sukunin iya biyan kuɗaɗen abinci, magunguna da kayan ayyuka daban-daban da ake buƙatar shigo da su a masana’antun mu. Wato dai irin matsalar tattalin arzikin da Sri Lanka ke fuskanta a yanzu kenan.
Maganar dai kai tsaye ita ce Najeriya na fuskantar mummunar matsalar ƙarancin kuɗi, ga wawakeken giɓin kasafin kuɗi, tulin basussuka da kuma taguwar da kuɗaɗen shigar da ƙasar ke samu ke yi a kullum.
Discussion about this post