Daraktan Tsare-tsaren Yaɗa Labaran Kamfen ɗin APC, Dele Alake, ya ce babu wani ma’aunin da za a iya kwakwanta bambancin mizanin nauyin Peter Obi na LP da kuma Bola Tinubu na APC.
Alake ya bayyana haka a lokacin da gidan talabijin na Channels ke tattaunawa da shi a ranar Laraba.
Ya ce Peter Obi wanda ya taɓa yin gwamna a Jihar Anambra, ya na baya can nesa fintinkau da Tinubu.
Ya ce Tinubu ya yi masa rata ta kowane fanni, ratar da ba zai iya cim masa ba.
Ya ce idan ana kwatanta kwarewa da cancantar zama shugaban ƙasa, ai Tinubu ko kaɗan ya fi ƙarfin a kwatanta shi da Peter Obi.
Da ya ci gaba da ragargazar Obi, Alake ya ce ai idan ma za a auna sauran ‘yan takarar da ke sahun gaba, wato Atiku, Tinubu, Kwankwaso da Obi, to Obi ɗin ne zai zo na ƙarshe wajen cancanta, gogewa da kuma ƙwarewa.
Alake ya ce hayagaga da hauragiyar ‘Obidients’ da magoya bayan Obi ke yi, iyakacin ta a soshiyal midiya kawai.
“Su kuma ‘yan hauragiya da jagaliyar soshiyal midiya, ba su ne ke zaɓe ba. Ɓaɓatun su ba shi da wani tasiri a zaɓe.” Inji Alake.
“Idan za a auna irin ayyukan da Obi ya yi lokacin da ya na gwamna da wanda Tinubu ya yi lokacin da ya na gwamna, sai kuma ci gaban da kowanen su ya haifar, to ai kowa ya san Tinubu ne shugaban da Najeriya ke ta santin ƙagara ta ga an samu domin ya ciyar da ƙasar gaba.” Inji shi.
“Yan soshiyal midiya fa ba wata tsiya ba ne, ba su ko zuwa wurin zaɓe ballanata su jefa ƙuri’a. Yawan su duk taron yuyuyu ne kawai.”
Discussion about this post