Bayanan abin da ya faru tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, a taron neman sulhun da su ka yi a Landan, a ranar Alhamis sun fito fili Premium Times ta damƙe.
An taron neman sulhu ɗin ne a otal ɗin Lane Carlton Hotel. Daga cikin zaratan ɓangaren masu goyon bayan Wike, waɗanda suka raka shi zaman sulhun akwai Gwamna Seye Makinde na Jihar Oyo, Samuel Ortom na Jihar Benuwai, Okezie Ikpeazu na Jihar Abiya. Shi kuma Atiku ya na tare da Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa.
Taron dai ya zo sa’o’i kaɗan bayan Wike ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kuma Shugaban Jam’iyyar LP, Peter Obi duk a Landan ɗin. Dama kuma a ranar Litinin ɓangaren Wike ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, wanda shi ma kamar Obi ya ke ƙoƙarin maida Wike ɓangaren sa, domin cin roba daga rigimar cikin gidan PDP, wadda ta rincaɓe tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani.
Majiyar PREMIUM TIMES ta ce ɓangaren Wike ya shaida wa Atiku cewa matakin farko kafin a daddale yin sulhu ɗin tukunna, har Wike ya goyi bayan Atiku, sai Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu ya sauka, a gaggauta maye gurbin sa da ɗan kudu.
Sun ce Wike da jama’ar sa ba za su taɓa goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa sannan kuma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa shi ma daga Arewa.
Ɗaya daga cikin gwamnonin ne ya yi magana a madadin sauran, ya ce wannan sharaɗi na farko su na so a gyara shi ne domin a yi adalci wajen rabon muƙamai. Kuma su na so a gyara da wuri kafin kusantowar zaɓen 2023.
Sannan kuma sun zargi Ayu da rarraba kai ko raba haɗin kan jam’iyya, maimakon kallon da ake yi masa wai wani mai haɗa kan PDP.
Ɓangaren Wike ya ce tun da aka kafa PDP ba a taɓa yin shugaban jam’iyya wanda ya rarraba kawunan ‘yan jam’iyya kamar Ayu ba.
Sun ce maimakon Ayu ya tashi ya nemi haɗin kan kowane ɓangare da sauran hasalallun da ba a yi wa adalci ba, sai ya ƙirƙiri sabon ra’ayin raba kawuna ta hanyar rungumar shugabannin da babu adalci da raba-daidai a cikin sa.
Wike dai ya zargi Ayu da nuna goyon bayan Atiku ƙarara a lokacin zaɓen fidda-gwani.
Ɓangaren Ayu ya ci gaba da cewa tilas Atiku ya tashi ya gyara rashin adalcin da aka yi wajen rabon muƙamai na shugabancin PDP, ta yadda tun a nan idan ya yi haka, to zai nuna da gaske ya ke yi zai iya haɗa kan ‘yan Najeriya kenan idan ya zama shugaban ƙasa.
Majiyar ta ce shi kuma Atiku ya yarda tabbas akwai ɓangarancin miƙa manyan muƙaman PDP a Arewa, to amma ya yi togaciya da cewa dokar PDP ta nuna idan shugaba ya sauka, ba za a iya yin gyaran da su ke so a yi ba, domin idan Ayu ya sauka, wanda zai maye gurbin sa ɗin ma Mataimakin Shugaban Jam’iyya ne na Ƙasa, kuma shi ma ɗan Arewa ɗin ne dai.
Sai dai kuma ɓangaren Wike sun tunatar da Atiku cewa a lokacin da shugaban PDP Okwesilieze Nwodo ya yi murabus cikin 2011 bayan an zaɓi Goodluck Jonathan ya zama shugaban ƙasa, ai ba a ɗauki mataimakin shugaban jam’iyya wanda shi ma a lokacin ɗan kudu ba ne.
Bayan an yamutsa gashin baki sosai a wurin taron, Atiku ya nemi su ɗan ba shi lokaci domin ya tuntuɓi manyan jam’iyya sannan ya waiwaye su.
Majiya ta ce wannan batun ne kaɗai aka tattauna a wurin taron, amma ba a tattauna sauran rashin jituwar da ke tsakanin Wike da Atiku ba.
Discussion about this post