Duk da yake ba wannan ne karon farko ba manyan makarantun Nijeriya musamman Jami’u samun kansu a irin wannan yanayin ba, na dogon yajin aiki, duk da kasancewa ya kamata a ce a cigaban dimokaradiyya irin wannan sha’ani na yajin aiki ya zama tarihi.
Bunkasar dimokaradiyya da kuma girman tattalin arzikin Nijeriya ya kamata a ce an samu wata hanya sahihiya ta magance matsalolin ilimi a Nijeriya, wanda ya hada hadda kyakkyawar mu’amala tsakanin ma’aikatan da kuma gwamnati, amma tabbas irin wannan dogon yajin aikin kauyanci ne a duniyar wannan zamani.
Ko shakka babu gwamnatotin Nijeria a kowane mataki basu bawa ilimi muhimmanci ba, musamma a lokacin da makarantu masu zaman kansu daga Primary zuwa Jami’a suka yalwata a kowane sako, sai ya zamanto shugabanni da attajirai suna Kura tsira da na bakinki, suka maida hankali kaiwa yayan su makarantun kudi, yanzu kan abin ma yayi gaba hatta karatun Jami’a shugabanni da attajarai sun gwammata sun kashe magudan kudi wajen kai yayan su kasashen wajen don nemo takardar degree.
Abin takaici da rashin hangen nesa, yau kasashe makotan mu irin kwatano, Togo da Ghana na samun makudan kudaden shiga da ga Nijeriya ta hanyar karatun jami’a.
Gazawar shugabanni Nijeriya ya fito fili a kan harkar ilimi, wadda ko da a wannan lokacin sai da Bankin Duniya ta gargadi Nijeriya a kan ta na sanya kashi 20% na kasafin kudinta a kan harkar ilimi.
KALUBALEN DA MALAMAN JAMI’OIN JAHOHI KE CIKI
A wannan lokaci za a iya cewa ma’aikatan jami’oin mallakar jahohi kamar suna tsaka mai wuya kasancewar kiraye-kiraye da kuma barazanar da gwamamnonin su suke yi musu a kan dole su koma aiki a bude jami’oi, domin suna ganin wannan rigima ce tsakanin gwmnatin tarayya da kuma ma’aikatan ta. Wannan yanayi tabbas zai saka wannan ma’aikata a tsaka mai wuya.
A waje guda kuma ita ASUU tana cewa, ita kungiyar ASUU ta duk malaman jami’a ce babu wani waraki, kuma duk abin da suke fada a kai ya shafi kowa da kowa, hasali wasu daga cikin abubuwan da suke fada a kai yafi shafi jami’oin jahohin ne ma, musamman revitalization da jami’oi da kuma promotion arrears da sauran su.
Ita kanta gwamntin tarayya ta nuna irin wannan wariya, a farkon tautanawar ta a kan sabunta yarjejeniyar 2009, gwamnati ta nuna cewa yarjejeniya a kan kara albashi, sai dai ta kai Tripartite Committee domin karin albashi ba kawai gwamntin tarayya zai shafa ba, har ma da na jahohi dama jami’oin masu zaman kansu.
Amma kungiyar ASUU ta bijire, domin ko Karin albashin ma’aikata da a kayi a 2019 sai da ya dauki wannan kwamiti kusan shekaru uku kafin su cimma matsaya N30K a matsayin mafi karancin albashi.
In zamu iya tunawa ko da a baya sai da Gwamnatin Tarayya tace, za ta sabunta albashin malaman jami’a amma kawai zai shafi jami’oin ta ne, ita bata da ikon tilastawa jahohi kara albashi, domin ba ta san karfin su ba. Amma kungiyar ASUU tace take kafa da kin aminta da hakan.
Babu shakka Jami’oin Jahohi suna cikin kaluballe a irin wannan yanayin, kuma in har matsin lamba ya sanya suka bijeriwa uwar kungiyar su ta ASUU a wannan yanayi da suke yaki mai mutukar sarkakiya, za su iya fuskantar kalubale kala-kala.
Zai yi wahala duk wata jami’a da ta janye daga wannan yajin aikin bata fuskanci dakatarwa ba daga cikin ita wannan kungiyar ba, har ma da cin tara yayin da za ta dawo cikin uwar kungiyar.
Ya zama dole, sai wadannan jami’oi sun yi nazari, kasancewar yadda Yan Siyasa musamman ma gwamnoni a Nijeriya wajen siyasantar da aikin gwamnati, hatta Karin albashi ko Karin girma sai sunga dama sukeyi, korar ma’aikata ba bisa ka’ida ba, kawo wasu tsare wanda yake tarwatsa tsarin ilimi ko makarantu ba wani kayan gabas bane a wajen gwamnonin wannan kasa.
A duk lokacin da ma’aikatan jami’oi ko malaman makaranta suka fuskaci irin wadannan matsaloli fa, sai sun bukaci kungiyoyin kwadago domin shiga tsakani da kwato musu yancin su.
A zahirance ma’aikatan jahohi sun fi fuskantar irin wadannan matsaloli, fiye da ma’aikatan tarayya, domin har yanzu akwai jahohin da basa iya biyan albashin dubu talatin duk da cewa yau sama da shekara uku da soma biyan wannan albashi.
Ya kamata shugabannin makarantu da kuma sauran masu ruwa a tsaki su fahimci muhimmancin kungiya a irin wannan lokacin, domin sune kadai kan tsayawa a kan hakkin mambobin su.
Zai yi wahalar gaske a ce Jami’oin jahohi sun fita daga kungiyar ASUU, fitar su ko bijeriwar umarnin kungiya kuwa ba karamin hadari bane a garesu yayin da suka fusakanci irin kalubalen a wajen jahohin su.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post