Akalla mutum 56 ne ‘yan bindiga suka kashe daga ranar 31 ga Yuli zuwa 6 ga Agusta a kasar nan.
Daga cikin yawan mutanen da suka mutu a makon jiya mutum bakwai jami’an tsaro ne sannan mutum 49 kuma mutanen gari.
Hakan ya auku a hare-haren da maharan suka kai har 13 a kasar nan inda a ciki akwai mutum 18 da aka kashe a karamar hukumar Wase jihar Filato.
PREMIUM TIMES Hausa ta tattara bayanan hare-haren da ƴan ta’adda suka gudanar daga rahotannin da kafafen yaɗa labarai yaɗa a cikin makon jiya.
Arewa ta Tsakiya
‘Yan bindiga Wanda ake zargin Fulani makiyaya sun kashe mutum 8 ‘yan gida daya sannan wasu mutum biyu sun ji rauni a kauyen Sanda Chugwi dake karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Wadanda harin ya auku a idon su sun ce maharan sun kai harin ne a cikin daren Lahadin da ta gabata.
Bayan haka a karamar hukumar Wase jihar Filato an kashe mutum 18 a jihar.
Mazaunan Wase sun tabbatar cewa mutum 16 daga cikin 18 din da aka kashe ‘yan bindiga ne sannan mutum biyu ‘yan kungiyar sa kai.
A karamar hukumar Ajaokuta dake jihar Kogi ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 14 ‘yan kasar India.
A harin da maharan suka kai sun kashe ‘yan kasar India biyu, ‘yan sanda biyu da direbobi biyu ‘yan Najeriya.
Kudu maso Gabas
Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa sannan sun jefa wasu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su daga saman gada cikin teku.
Wannan abin tashin hankali ya auku ne a kauyen Alor dake karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.
A unguwar Umuafom dake kauyen Orogwe a karamar hukumar Owerri ta Yamma jihar Imo ‘yan bindiga sun kashe mutum 7.
Maharan sun afka kauyen da misalin karfe 9:30 na daren Litinin.
Sannan rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar cewa ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda hudu a jihar ranar Asabar.
Maharan sun kashe jami’an tsaron ne a kauyen Agwa Dake karamar hukumar Oguta.
Kudu maso Yamma
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta bayyana cewa a ranar Talatar makon jiya ‘yan sanda sun tsinci gawar wata mata dake da shekara 65 da ake cigiyarta a kauyen Ilesa.
Jami’an tsaron sun tsinci gawar matan a gonan ta amma kuma an kwakule daya daga cikin idonta.
A jihar Osun ‘yan bindiga sun kashe wani dan kungiyar asiri mai suna ‘Eye’ Tajudeen Rabiu mai shekara 42 a Kofar shagon matarsa dake Osogbo.
Bayan haka a jihar Oyo ‘yan bindiga sun kashe dalibar Jami’ar Ladoke Akintola LAUTECH dake Ogbomoso Rachael Opadele da wani Olugbenga Owolabi da suka yi garkuwa da ita bayan an biya su kuɗin fansa.
Arewa maso Yamma
‘Yan bindiga sun kashe mutum daya kuma sun yi garkuwa da shugaban kwalejin koyar da lissafi dake Manchok a karamar hukumar Kaura, jihar Kaduna.
Arewa maso Gabas
Ƴan bindiga sun kai wa jerin gwanon motocin Mataimakin sifeto Janar ‘yan sanda na Zone 12 dake Bauchi Audu Madaki inda ya ji ciwo sannan Dan sanda daya ya mutu.
Discussion about this post