Rundunar sojin sama da ƙasa dake aiki a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sun kashe mahara sama da 45 a cikin makonni biyu da suka gabata.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka da yake bayani kan nasarar da sojoji suka samu akan ƴan ta’adda.
Onyeuko ya ce a Arewa ta Tsakiya rundunar sojin sama dake aiki karkashin ‘Operation Whirl Punch’ sun kashe gogarman ƴan bindiga Alhaji Shanono a kauyen Ukambo dake jihar Kaduna.
Ya ce sojojin sun Kai wa maharan hari ne yayin da suke taro a ranar 8 ga Agusta.
Onyeuko ya ce rundunar sojin sama ta kashe Shanono da wasu mahara 18 a harin da suka Kai wa maharan sannan sun kwace bindigogi Kirar AK-47 30 da babura 30.
Ya ce bayan haka sun ceto mutum 45 waɗanda maharan suka yi garkuwa da su.
Onyeuko ya ce rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ ta kama wasu mahara da ake nemansu ruwa a jallo.
Ya ce dakarun sun kama Nathaniel Azege Wanda ya dade yana damun mutane a garin Makurdi, da wani Moses Aindigh mai shekara 27 da Iluyasu Mohammed mai shekara 37 a duk a wannan farmaki.
A yankin Arewa maso Yamma a ranar 25 ga Yuli Onyeuko ya ce ‘Operation Hadarin Daji’ sun kama mutum biyar da ake zargi ‘yan bindiga ne da suka hada da Muritala Wada, Saminu Sani, Shamisu Adamu, Salisu Saadu da Usman Ibrahim a kauyen Jibia dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Ya ce rundunar sojin sama dake aiki a karkashin ‘Operation Hadarin Daji’ a ranar 6 ga Agusta sun kai wa ‘yan bindiga hari maboyar su dake dajin Rugu.
Onyeuko ya ce an kashe shugaban ‘yan bindiga Wanda sojojin suka dade sun nema ruwa a jallo Alhaji Abdulkareem Lawal Wanda aka fi sani da Abdulkareem Boss da maƙarraban sa.
“Bayanan da dakarun suka samu ya nuna Abdulkareem Boss ya dade yana kai wa mutane hari, satan dabbobi, yin garkuwa da mutane sannan da hada hannu da wasu maharan domin kai wa mutane hari.
“Abdulkareem Boss ya kashe sojin ƙasa guda 27.
Onyeuko ya ce daga ranar 31 ga Yuli zuwa 2 ga Agusta dakaru sun kama Malam Yahaya wanda ke hada baki da mahara ana Kai wa mutane hari.
An daɗe ana farautar Yahaya kafin Allah ya sa ya shiga hannu.
Sojoji sun kwato shanu 161, rakuma 8 da babban daurin kaya daga maharan bayan sun ragargaza su a Zango a karamar hukumar Shinkafi.
Discussion about this post