Kakakin kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Abdulmumini Jibrin ya kalubalanci ƴan siyasan jihar Kano cewa Rabiu Kwankwaso ya shiga gaban su ko suna so ko basu so.
Da yake tattaunawa da Talbijin ɗin Arise, Jibrin ya bayyana cewa jarumtaka da iya siyasar Kwankwaso ta nuna a zaɓen 2019 inda shi kadai tilo ya yi wasan kura da duk wani ɗan siyasa a Kano kuma kowa ya gani.
” A 2019, duk wanda yake ji da kansa a siyasar Kano duk mun bi Ganduje ne, Barau Jibrin ne, Shekarau ne, Kabiru Gaya, Kawu Sumaila, duk mun yi wa APC aiki ne amma Kwankwaso ya yi ragaraga da mu ya ci zaɓe, kawai an hana shi ne.
” Sakamakon da aka bayyana kawai an bayyana haka ne amma Kwankwaso da ɗan takarar sa ya ci zaɓe wannan kowa ya san haka.
Wannan shine amsar da ya baiwa Sheun na Channels da ya tambayeshi kan zawarcin da ake yi wa Shekarau da ga wasu jam’iyyun ya wancakalar da NNPP.
Jibrin ya kara da cewa, idan ma haka ne, Kwankwaso dai ba kanwan lasa bane, ya isa kowa riga da wando a Kano, koma shi kaɗai gayya ne.
Idan ba a manta ba, Shekarau ya fice daga jam’iyyar APC ya koma NNPC a farkon bayan sabani da ya samu da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje kan bangaren da zai shugabanci APC a jihar.
Wannan rashin jituwa ya kai su har kotun koli, wanda a karshe ta baiwa ɓangaren Ganduje shugabancin jam’iyyar.
Discussion about this post