Yayin da Najeriya ke fama da matsanancin ƙuncin rayuwa, tsadar kayan abinci, hare-haren ‘yan bingida da na ‘yan ta’adda, manyan ‘yan siyasa musamman gwamnoni da manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati sun maida hankali wajen sharholiyar zuwa ƙasashen Turai da sunan yin taron ganawa da juna a can.
Sun maida Turai dandalin zuwa yin tarukan tuggu, kisisina, maƙarƙashiya, ƙumbiya-ƙumbiya, kutunguila da algungumancin yadda za a ci zaɓen 2023, wanda shi ne a gaban su kaɗai.
Tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani cikin Yuni, fitattun ‘yan siyasa da dama su ka fara karakainar tafiya ƙasashen Turai domin tsare-tsaren yadda za su ci zaɓen shugaban ƙasa.
Aƙalla dai an yi tarukan gungu uku na ‘yan siyasa cikin wannan makon a Landan. Kuma dukkan tarukan sun haɗa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, wanda ke jagorantar rundunar tawaye a PDP tun bayan da Atiku Abubakar ya kayar da shi a zaɓen fidda gwani.
Taron baya-bayan nan da aka yi da Wike da Atiku da wasu gwamnoni, kafin shi ma kwanaki uku an yi wani taron tsakanin Wike da tawagar sa da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da kuma ɗan takarar LP Peter Obi.
Kafin nan kuma sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu a ranar da su ka gana da Obasanjo ɗin, duk a Landan.
Tawagar Tinubu ta ƙunshi Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da kuma Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti.
Kafin zugar tafiya Landan taron tuggu, rundunar Wike ta je Turkiyya cikin watan Yuni, domin yin abin da wani hadimin sa ya ce, “tsare-tsaren shirya alƙiblar da Wike zai fuskanta”, yayin da rikici ya kunno kai tsakanin sa da Atiku.
Ba Wike da rundunar sa kaɗai ke karakainar zuwa ƙasashen Turai ba tun cikin Yuni, Tinubu ya je Faransa kuma ya je Birtaniya. Atiku kuma ya ma daɗe ya na karɓar baƙuncin rundunar sa a Dubai, birnin da ya je ya yi kwanciyar sa tun bayan faɗuwa zaɓen 2019 da ya yi.
Masifar Tsadar Dala Ba Ta Firgita Su: Waɗannan manyan ‘yan siyasa da talakawa ke tunanin su ne za su ceto su daga ƙuncin rayuwa, su na karakainar kashe maƙudan kuɗaɗe zuwa Turai a daidai lokacin da dala ke masifar tsadar, darajar naira kuma ta faɗi warwas a bankuna da kasuwannin ‘yan canji.
Haka nan kuma a lokacin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke rabawa a kowane wata ya ragu sosai, gwamnonin jihohi sun dogara da ciwo bashi da ɗaukin gwamnatin tarayya domin biyan albashi, a lokacin da biyan haƙƙin ‘yan fansho ke gagarar jihohi masu yawa.
Rahoton watan jiya ya nuna jihohi 36 kowace ana bin ta ɗimbin basussuka na haƙƙin ‘yan fansho da garatutin da ta kasa biya.
Gwamnatin Abiya ta kasa biyan garatutin shekaru 20 da fanshon shekaru 38, sannan malaman Jami’ar ABSU na bin albashin watanni 10, na Kwalejin Fasaha na bin na watanni 30.
Haka ake fama a Jihar Adamawa, Benuwai, Legas da Ekiti wajen kasa biyan haƙƙin garatuti.
Wani mai suna Lanre da ya ragargaje su a soshiyal midiya, ya ce “duk kwana ɗaya a otal ɗin Carlton da Jumeirah naira 500,000 ake biya. Don haka ba shugabanni ba ne, dillalai ne dai kawai.”
Discussion about this post