Bagudu, wanda gwamna ne a Jihar Kebbi, a zamanin mulkin soja na marigayi Sani Abacha ya kasance babban gogarman yi wa kuɗaɗen da aka sata daga aljihun gwamnati lodi da jigilar su zuwa kasashen waje.
PREMIUM TIMES ta gano cewa a ranar Laraba ɗin nan Ibrahim Bagudu a madadin Atiku ya cimma yarjejeniyar sasantawa da Amurka ba sai an ci gaba da shari’ar ba.
Ma’aikatar Shari’ar Amurka ce ke wakiltar ƙasar, yayin da aka sanar wa Kotun Tarayya ta Washington batun sasantawar da su ke son yi.
A ranar 3 Ga Agusta ɓangarorin biyu su ka shiga da ba’asin shirin yarjejeniyar a Kotun Gundumar Columbia.
Shugaban Kotun John Bates, ya karɓi uzirin su, kuma ya nemi ɓangarorin biyu su sanar da shi a rubuce irin yarjejeniyar da su ka cimma nan da ranar 2 Ga Nuwamba. Idan ma sun kasa cimma yarjejeniyar, su sanar da shi.
Gogarma Atiku Bagudu shi ne sahun gaba wajen dillancin karkatar da yawancin dala biliyan 3.6 da aka maido Najeriya daga kuɗaɗen da aka sace aka ɓoye waje zamanin Abacha. An maido adadin kuɗaɗen dala biliyan 3.6 daga 1998 zuwa yau.
Tun cikin 2003 ake kwatagwangwamar shari’a da Bagudu a Amurka.
Kuma PREMIUM TIMES ta riƙa buga yadda Amurka ta kafa masa ƙahon zuƙa, har ta kai an tsare Bagudu a Amurka cikin kurkuku tsawon watanni shida.
Cikin watan Mayu PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton musamman kan sata da jidar kuɗaɗen da su Bagudu su ka riƙa yi a zamanin mulkin Abacha.
Hukumar Daƙile Manyan Laifukan Zamba ta Birtaniya (NCA) ta bayyana ƙwato dala miliyan 23.5 waɗanda aka sata daga Najeriya lokacin mulkin sani Abacha.
An ƙwace kuɗaɗen daga hannun ɗan da Mohammed Abacha da kuma wani kamfanin gare mai suna Mecosta Securities Inc.
Haka dai Hukumar Daƙile Manyan Laifukan Zamba ta Birtaniya (NCA), ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Binciken ƙwaƙwaf ɗin da PREMIUM TIMES ta ƙara yi kan wasu kwafen takardun bayanai sun nuna asusun ajiyar kamfanin Mecosta na Landan, wanda aka bankaɗo kuɗaɗen satar a ciki, asusun na Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ne ke kula da shi.
A cikin shekarun 1990s Bagudu ya zama wani dillali, ɗan kamasho kuma mai lodi da jigilar maƙudan kuɗaɗen da Abacha ke karkatarwa ƙasashen waje. Bagudu ake bai wa kuɗaɗen ya na kimshewa a can.
A ranar 5 Ga Mayu, Hukumar NCA ta Birtaniya ta bayyana cewa Gwamnatin Birtaniya ta ƙara bankaɗo dala miliyan 23 da makusanta da iyalan Abacha su ka sata, su ka ɓoye a Ingila.
Hukumar Daƙile Laifuka ta Birtaniya ta bayyana bankaɗo waɗansu kuɗaɗe har dala miliyan 23.5, waɗanda aka tabbatar makusanta da iyalan tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, marigayi Sani Abacha ne su ka saci kuɗin daga Najeriya su ka ɓoye a Ingila.
An gano kuɗaɗen waɗanda su na daga cikin maƙudan kuɗaɗen Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce an shafe shekaru a cikin 1990s ana jida daga Najeriya ana ɓoyewa ƙasashen waje.
Hukumar Daƙile Laifuka ta Birtaniya ta ce Abacha ne da makusantan sa da iyalan sa su ka riƙa kinshe kuɗaɗen a waje.
Haka dai hukumar ta bayyana a shafin ta na yanar gizo a ranar Alhamis.
Tsare Atiku Bagudu A Kurkukun Amurka:
Cikin 2003 an bankaɗo dala miliyan 163 a hannun Bagudu a Jersey, har aka tsare shi watanni shida. Ya cimma yarjejeniya da masu gabatar da ƙara aka maido kuɗaɗen Najeriya, shi kuma ya nemi kada a maida shi Najeriya, tunda ya biya kuɗaɗen.
PREMIUM TIMES HAUSA ta taɓa buga labarin ɗaure Bagudu a kurkukun Amurka, saboda mahukuntan ƙasar sun gano ƙasurgumin ɓarawon kuɗaɗen gwamnatin Najeriya ne.
Sannan kuma dala miliyan 308 da aka bankaɗo cikin 2020, su ma Atiku Bagudu ne ya karkatar da su.
Atiku ya yi tsamo-tsamo cikin harƙallar karkatar da ƙananan biliyoyin dalolin satar Abacha a bankunan ƙasashen Virgin Islands, Ingila, Guensey da Jersey.
Discussion about this post