Sanata Ahmed Babba-Kaita mai wakiltar Shiyyar Daura wato Katsina ta Tsakiya na ci gaba da yi wa siyasar yankin haɗiyar mesa, tun bayan ficewar sa daga APC, Jam’iyyar da aka zaɓe lokaci ɗaya da Shugaba Muhammadu Buhari.
Kaita dai ya koma PDP inda tuni ya kafa ofishin kamfen ɗin sa a tsohon ofishin kamfen ɗin Buhari a cikin garin Daura.
Ofishin dai nan ne Buhari ya kafa ofishin TBO cikin 2002, lokacin da ya shiga siyasa a APP, har ya fito takarar shugaban ƙasa cikin 2003 a karon farko.
Kaita ya fice daga APC ya koma PDP cikin watan Afrilu. Ya zargi Gwamna Aminu Masari da laifin ƙin bai wa manyan ‘yan jam’iyyar su damar faɗa a ji da damammaki da dama. Kuma ya zargi Masari da ƙin yin zaɓen ƙananan hukumomi da kuma bijire wa tsarin dimokraɗiyya.
Haka shi ma ɗan uwan Buhari kuma wakilin na shugaban ƙasa a Majalisar Tarayya, mai wakiltar Sandamu/Daura/Mai’aduwa, Fatuhu Muhammad shi ma ya fice daga APC.
Har yanzu bai bayyana jam’iyyyar da zai koma ba, amma dai ana zaton PDP zai koma.
Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Sanata Babba-Kaita ya sayi ofishin ne cikin makon jiya, kuma ya biya mai shi kuɗin sa lakadan.
Kafin nan dai ofishin ya kasance wurin da manyan ‘yan siyasar Daura ke hada-hadar siyasa tsawon shekaru da dama.
Bayan Babba-Kaita ya sayi ofishin, sai ya damƙa shi ga PDP ya ce ya kasance ofishin jam’iyyyar a Ƙaramar Hukumar Daura.
“Gaskiyar mana an kai munzilin da a yanzu ba mu iya riƙe ofishin. Shi ya sa mu na ji mu na gani ya fi ƙarfin mu, mu ka haƙura.” Inji wani jigon APC kuma tsohon ɗan TBO.
“Amma dai abin akwai takaici,a ce wurin da mu ka riƙa a matsayin wani ruhin tafiyar siyasar mu, a ce mun kasa riƙe.”
PREMIUM TIMES ta gano cewa ofishin mallakar wani tsohon ɗan majalisar tarayya mai suna Salisu Ado ne ke da shi, kuma ya bayar da shi matsayin odishin Tafiyar Siyasar Buhari (The Buhari Organisation), ba tare da ana biyan ko sisi ba.
“Wurin ya koma na marayu bayan mai wurin ya rasu. Mu kuma cikin makusantan Buhari aka sara wanda zai taimaka mana ya sayi wurin. Sai waɗanda su ka ci gadon ofishin, su ka sayar wa Babba Kaita.”
Wani da ke cikin waɗanda su ka yi dillancin cinikin ya ce sun yi wa mutanen TBO tayin ko za su sayi ofishin, amma su ka kasa.
Hadimin Ɗan Majalisar Tarayya Fatuhu Mohammed, mai suna Ahmad Ganga, ya shaida wa wakilin mu wa kafin Fatuhu ya fice daga APC shi ke biyan naira 500,000 duk wata domin hidimar jam’iyya, ciki har da kula da ofishin na TBO a Daura.
Wani da aka kafa TBO tare da shi a Katsina mai suna Muntari TBO, ya ce wa wakilin mu ai sayen filin da Babba Kaita ya yi, ba wata bajinta ba ce, nuna isa ce kawai irin isar-ƙadagi domin ya burge mutane.
Wani hadimin Gwamna Masari ya ce TBO ta cika burin dalilin kafa ta bayan da Buhari ya zama shugaban ƙasa.
Discussion about this post