Gwamnatin Tarayya ta ƙaƙaba tarar naira miliyan 5 ga Trust TV, gidan talbijin na yanar gizo, mallakar kamfanin jaridar Daily Trust.
An ƙaƙaba masa tarar watanni masu yawa bayan watsa wata tattaunawa da ya riƙa yi daki-daki da aka riƙa nuno hira da ‘yan bindiga, musamman Kachalla Turji da ke dajin Zamfara.
Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) ce ta ƙaƙaba tarar, kamar yadda wata sanarwa daga hukumar ta tabbatar.
Tuni dai ake ta maida wa NBC maida wa NBC kakkausan raddi daga ƙungiyoyi daban-daban na kare haƙƙin jaridu da ‘yancin buga labarai.
An ƙaƙaba tarar ce kwana kaɗan bayan Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya za ta hukunta Trust TV da BBC saboda sun yaɗa hirarrakin da su ka yi da ‘yan ta’adda.
Cikin waɗanda su ka ragargaji gwamnati har da ƙungiyar SERAP.
Shugaban Hukumar NBC Balarabe Shehu Illela ne ya sa hannu kan wasiƙar da aka aika wa Trust TV, inda a cikin wasiƙar ya ce abin da Trust TV ta yi ya karya dokar kiyaye yaɗa labarai ta ‘NBC Code.’
“Yayin da mu ke nazarin lamarin, ya na da kyau a matsayin mu na gidan talabijin mun tabbata mu na aiki ne don jama’a. A sani cewa maganar ‘yan bindiga lamari ne mai sarƙaƙiya kuma ya shafi miliyoyin jama’a.” Haka Trust TV ta bayyana a ranar Laraba.
NBC dai ta ƙaƙaba tarar kan wani bidiyo da Trsut TV ta wallafa ranar 5 Ga Maris, 2022.
Bidiyo ya taɓo salsalar faruwar rikici tsakanin makiyaya da manoma, wanda ya yanzu ya canja salo kuma ya ƙara muni a Najeriya.
Bidiyon ya yi zurfin bayanai kan rashin adalci, ƙabilanci da rashin ingantacciyar gwamnati cewa su ne su ka sa rikicin ya kai munin da ake fama da shi a yanzu.
Rahoton ya kuma saka muryoyin wasu masana kan abin da ya dace a yi domin magance gagarimar matsalar, ciki kuwa har da shi kan sa Ministan Yaɗa Labarai, Kai Mohammed da Sanata Sa’idu Ɗansadau daga Jihar Zamfara, yankin da ‘yan bindiga su ka fi kaka-gida.
Haka kuma an yi hira da Farfesa Abubakar Saddique na Jami’ar Ahmadu Bello, Dakta Murtala Ahmed Rufai na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto, waɗanda su ka shafe shekaru su na nazarin ‘yan bindiga.
Bidiyon kuma ya bayar da ƙarin haske kan irin wahala da azabar da jama’a su ka ɗanɗana, ta asarar dukiya, rayuka da maƙudan kuɗaɗe.
Discussion about this post