Bataliyar Sojojin Gamayyar ‘Operation Haɗin Kai’ ta 2, ta Arewa maso Gabas, ta kafa kwamitin binciken yadda aka kashe fitaccen malamin nan Sheikh Goni Gashuwa a ranar Juma’a.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Sojoji Anyanwu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce tuni kwamitin har ya fara aiki domin tabbatar da an gano musabbabin kisan tare da hukunta duk wani mai hannu a wannan aika-aika.
Ya ce kwamitin na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe.
“Biyo bayan labarin kisan malamin, Sheikh Goni Gashuwa da jaridar PREMIUM TIMES ta buga, mahukuntan sojoji sun kafa kwamitin binciken musabbabi da kuma hukunta duk wanda ke da hannu a ciki.” Inji sanarwar.
A wata sabuwa kuma, PREMIUM TIMES ta ƙara bankaɗo cewa ashe sojan da ya yi kisan tsohon ɓarawo ne, kwamandan sa ya taɓa tsine masa.
John Gabriel, sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe, an tabbatar da cewa tsohon ɓarawo ne, wanda aka taɓa zargin ya saci kuɗin Kwamandan Bataliya ta 241 da ke Nguru, har naira 480,000.
Majiyar PREMIUM TIMES a cikin sojoji ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an maida Gabriel zuwa shingen binciken motoci ne bayan an kama shi ya yi satar kuɗin ogan sa har sau biyu.
Na farko naira 80,000 ne aka nema sama ko ƙasa, aka rasa. Karo na biyu kuma cewar majiyar, naira 400,000 ne su ka ɓata. “Lokacin Gabriel, wanda Lance Kofur ne, shi ne dogarin Kwamandan Bataliya ta 241, ta Sojojin Nguru.
“Daga nan Kwamandan mai suna GS Oyemole ya sallame shi, aka maida shi tsaron hanya. Amma kafin ya sallame shi, sai ta ya tsine masa, saboda ya tabbatar shi ne ya ɗauki kuɗin, amma kuma ya rasa shaidar da zai iya kafa masa. Shi ne ya tsine masa, kuma ya ce zai yi mummunan ƙarshe.
“Ai kuwa an kama Gabriel da laifin kisa ne a ranar da Kwamandan da ya yi wa sata ya miƙa ragamar jagoranci a hannun wanda ya canje shi.”
Majiya ta ce su Gabriel su na da wani guruf da su ke shirya ɓarna. Kuma ya bindige malamin ne saboda ya ga wani tulin abu a cikin motar, wanda ya yi zaton kuɗi ne.
Jama’a Su Kwantar Da Hankali, Za A Yi Bincike Da Hukunci -Gwamna Buni:
A na shi ɓangaren, Gwamnan Mai Mala-Buni na Jihar Yobe ya nuna takaici tare da yin Allah-wadai da kisan malamin.
Cikin wata takarda da Jami’in Yaɗa Labaran Gwamna, Mahmud Mohammed ya fitar, Gwamna Buni ya ce kisan babban abin takaici ne, kuma dabbanci ci ne.
Bayan ya yi wa iyalan mamacin da sauran ‘yan Jihar Yobe ta’aziyya, ya ce za a yi bincike, kuma za a hukunta masu hannu a kisan.
Daga nan ya yi kira da a kwantar da hankula.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kisan da kuma cewa ‘yan sanda sun damƙe sojoji biyun da ake zargi.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta bada tabbacin cewa ta damƙe sojoji biyu da ake zargin su da hannu wajen kashe fitaccen malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh Goni Gashuwa.
An kashe Sheikh Goni ne a ranar Juma’a da dare bayan ya wuce Nguru.
Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargi da kisan malamin sojoji ne guda biyu, kuma tuni su na hannun ‘yan sanda.
Sai dai kuma ya ce lokaci bai yi ba da za a yi gaggawar fitar da bayanai tukunna.
“Da zaran an natsa wajen bincike cikin ‘yan kwanaki za a sanar da komai.
Sai dai kuma rundunar ‘yan sandan ta Yobe ba ta bayyana sunayen sojojin da aka kama ba.
Majiya ta ce farkon lamarin dai wani soja ne ya tsayar da Sheikh Goni bayan ya wuce Nguru.
“Bayan ya wuce Nguru ne kuma sai ya tsaya domin ya yi fitsari. Bayan Sheikh da gama ya nufi mota, sai sojan ya nuna shi da bindiga, ya ce idan ya matsa zai harbe shi. Kuma nan take ya harbe shi.
“Bayan sojan ya bindige malamin, sai ya nemi tayar da motar malamin ya gudu, amma mota ta ƙi tashi. Daga nan ne kuma ya kira soja na biyu.
“Da soja na biyu ya zo ne, sai suka ga ashe motar ma ta ci karan-shaf. Sai su ka kira ‘yan bijilante don su je su taya su kiciniya.
“Ana cikin kiciniyar motocin biyu ne, sai ‘yan bijilante su ka ga ɗaya motar da jini a jikin ta. Bayan sun duba sai su ka ga gawar Sheikh Goni a cikin daji. Daga baya su ka kai rahoto wurin ‘yan sanda.”
Mataimakin Sufurtandan ‘Yan Sanda kuma Kakakin su na Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya ce sun amsa laifin da ake tuhuma.
Ya dai ce za a bayyana komai idan an kammala bincike.
Wannan ne karo na uku da haka ta faru da jami’an tsaro a Jihar Yobe.
Discussion about this post