Yayin da har yau ba a gama fitar da mutanen da bene hawa uku ya rufta kan su a kasuwar wayar GSM ta titin Beirut Road da ke Kani ba, tabbatar da mutuwar mutane biyu, inda ɗaya wutar lantarki ce ta kashe shi a ƙoƙarin aikin ceton waɗanda gini ya rufta a kan su.
Wanda wutar lantarkin ta kashe dai jami’in Hukumar Wutar Lantarki ta Jihar Kano ne (KEDC), kamar yadda Sakataren Ƙungiyar Red Cross ta Jihar Kano, Musa Abdullahi ya tabbatar.
Ya ce ma’aikacin ya rasa ran sa a lokacin da ya ke ƙoƙarin datse wutar lantarki daga jikin benen da ya rufta.
Ya zuwa Magaribar ranar Talatar da abin ya faru, wasu mutanen da su ka yi dafifi a wurin da abin ya faru sun riƙa nuna damuwar cewa an samu jinkiri kafin masu ceto su isa wurin da benen ya rufta.
“Yanzu haka ana buga wayar wani daga cikin waɗanda ginin ya rufta masu, amma ceton su ya gagara.” Inji wani.
Hukumar Agajin Gaggawa NEMA ta ce an ceto mutum takwas, an garzaya da su Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed.
Kakakin NEMA Manzo Ezekiel ya ce sun samu ƙananan raunuka, an duba su an sallame su. Amma ɗaya mai raunuka ya mutu. Ɗaya kuma mai karaya da dama ya na ci gaba da jiyya. Ya ce ana ci gaba da aikin ceto.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya jajanta wa waɗanda Ibtila’in ya ritsa da su.
Yayin da ya ce za a kafa kwamitin bincike, Ganduje ya ɗage taron rantsar da sabbin kwashinonin da ya naɗa kwanan baya.
Sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai Mohammed Garba ya sa wa hannu, ta ce Ganduje ya ɗage rantsarwar domin jihar ta yi jimamin waɗanda ginin ya rufta kan su.
Discussion about this post