Rikicin cikin gida da ya dagula jam’iyyyar PDP a Kano sai ƙara muni ya ke yi, yayin da Mohammed Abacha ya ke ci gaba da iƙirarin cewa shi ne dai halastaccen ɗan takarar gwamna da jam’iyyyar PDP ta tsayar.
Mohammed wanda ɗa ne ga tsohon Shugaban Mulkin Soja Sani Abacha, wani bangaren PDP ne ya zaɓe shi ɗan takarar gwamna, yayin da ɗaya ɓangaren kuma su ka zaɓi Sadiq Wali.
Sai dai kuma uwar jam’iyyya ta ƙasa ta amince da Wali ne ɗan takarar gwamna ba Mohammed Abacha ba.
Ita ma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, wadda ta je ta sa-ido ta ga yadda zaɓen da ɓangaren Mohammed Abacha su ka gudanar ya wakana, daga baya ta jingine shi, ta koma ta ce Wali ne halastaccen ɗan takara.
Daga nan ne kuma INEC ta maye gurbin Mohammed Abacha da sunan Sadiq Wali.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mohammed Yakubu, ya ce INEC ta cire sunan Mohammed Abacha ne ta maye gurbin sa da na Sadiq Wali, bayan da PDP ta nuna wa hukumar umarnin kotu, wanda hukuncin Mai Shari’a ya nuna cewa ɓangaren PDP da ya zaɓi Sadiq Wali ne halastaccen ɓangaren PDP, ba ɓangaren Mohammed Abacha ba.
“Mun je sa idon duba zaɓen da ɓangaren Mohammed Abacha su ka gudanar, amma kuma daga baya PDP ta gabatar mana da hukuncin kotu da ya nuna bangaren Wali ne halastaccen ɗan takara.” Inji Yakubu Shugaban INEC, yayin da ya kai ziyara Kano, a ranar Alhamis.
“Ina ganin an warware matsalar a cikin jam’iyya, saboda jam’iyya ce ke da alhakin miƙa wa INEC sunayen ‘yan takara, ba aikin INEC ba ne.”
Sai dai kuma ɓangaren kamfen ɗin Abacha sun ce PDP ta yaudari INEC, ta yi wa hukumar dodorido da sunan Sadiq Wali, wanda kwata-kwata ba shi ba ne INEC ta je zaman shirya zaɓen fidda gwanin da ya ci takarar fidda gwani ba.
Haka dai Kakakin Kamfen ɗin Mohammed Abacha, Manniru Mailafiya ya bayyana.
“Ai Sashe na 84(1) na Dokar Zaɓen 2022, cewa ya yi: “jam’iyyar da ke son tsayar da ɗan takara a ƙarƙashin wannan doka, to tilas ta shiga zaɓen fidda gwanin ‘yan takara na dukkan muƙaman da ta ke so ta shiga zaɓen su. Kuma tilas ne sai INEC ta kalli yadda zaɓen ya gudana.” Inji Mailafiya.
“Don haka mu na sanar da duniya cewa Mohammed Abacha ne halastaccen ɗan takarar PDP na zaɓen gwamnan Kano, a zaɓen 2023. Kuma shi ne wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da zaɓen sa.
“A zaɓen da Mohammed Abacha ya yi nasara, Kwamishinan Zaɓe na Kano ya aika da wakilan sa, waɗanda su ka kalli yadda zaɓen ya gudana, bisa yadda Sashe na 84 Na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar. Kuma ya sanar wa duniya cewa PDP a ƙarƙashin shugabancin Shehu Sagagi a Kano ta zaɓi Mohammed Abacha ya yi mata takarar gwamna a zaɓen 2023.”
Mailafiya ya ce duk wani ba’asi da uwar jam’iyya ta miƙa wa INEC, shirme ne kawai don don a yamutsa jam’iyya ta hanyar haifar da ruɗani, a cikin ta.
“Don haka mu na kira ga Shugaban INEC Mahmood Yakubu ya sake bin takardar kotun da PDP ta aika masa, a ciki zai ga Sadiq Wali ko takarar zaɓe bai shiga ba. Saboda haka INEC ta gaggauta cire sunan sa, ta maye gurbin sa da na Mohammed Abacha ɗin da ta cire.
Discussion about this post