Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya bayyana cewa babu wata hujjar da Gwamnonin Najeriya ke da ita da za ta hana a fara cirar kuɗaɗen su a biya masu haƙƙin da za a bai wa kuɗaɗen su.
Malami ya shaida wa manema labarai haka a Fadar Shugaban Ƙasa haka wurin taron ganawa da ‘yan jarida, wanda Ministoci ke yi cewa “surutai da maganganun da gwamnoni ke yi ba su da wani dalili.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda cikin wannan makon Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed cewa ta dakatar da fara cirar kuɗaɗen tukunna, har sai an ga hukuncin da kotu ta yanke.
Kamar yadda Gwamnonin Najeriya ke cewa haƙƙin da dillalan gidogar ke neman a biya ya daɗe ba a lokacin su abin ya faru ba, kuma babu takamaimen hujjojin da ke nuna an yi ayyukan da su ka ce sun yi a ƙananan hukumomi 774, to shi ma Malami ya ce rigimar gadon ta ya yi, tun kafin ya zama Ministan Shari’a ya ke rikicin.
Malami ya ce tun asali Gwamnoni ne su ka zauna su ka nemi wasu kamfanoni su yi masu wasu ayyuka da za a cire kuɗaɗen daga kuɗaɗen Paris Club. Saboda haka waɗannan jami’an tuntuɓa gwamnoni ne da kan su su ka nemi su yi masu ayyukan a lokacin.”
Ya ce lokacin da aka samu nasarar maido wa gwamnoni kuɗaɗen Paris Club, sai gwamnoni su ka damƙa wa gwamnoni su ka damƙa wa gwamnatin tarayya cakin kuɗin da su ke so a cira da asusun su a biya jami’an tuntuɓar.”
Malami ya ce Gwamnonin Najeriya sun yarda an yi masu ayyukan kenan, tunda har ma sun fara biyan su kuɗaɗen, amma daga baya sai su ka daina.
“Wannan ne ya sa jami’an tuntuɓar su ka garzaya kotu, har gwamnonin su ka nemi a sasanta a wajen kotu.
Malami ya ce kotu ta bada umarnin a fara cirar kuɗin bayan an sanar da Gwamnatin Buhari, sai gwamnati ta bi umarnin kotu, har Buhari ya damƙa bayanan a ofishi na.
Ya ce ana cikin haka sai aka samu canjin Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, inda daga nan rigimar ta koma ɗanya sharaf.
Sai dai kuma an dakatar da biyan a yanzu, saboda Gwamnonin Najeriya sun nuna wa Buhari cewa rigimar ta na kotu.
Matsayar Malami Tun A Cikin 2021:
Rigimar Gada-gadar Dala Miliyan 418: Malami Ya Ce Tilas Gwamnoni Su Biya ‘Yan Gada-gada’ Tsabar Kuɗaɗen:
Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya shaida wa Gwamnoni 36 na Najeriya cewa alƙalami ya bushe, tilas sai sun biya ‘yan gada-gadar kwangila dala miliyan 418 ɗin da hukuncin kotu ya gindaya masu.
Malami ya ce saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta fasa fara cire dala miliyan 418 a hankali ba ta na dannawa asusun ‘yan gidogar, domin kotu ce ta yanke hukuncin cewa a biya su kuɗaɗen.
Kakkausan kalaman Malami sun zo ne mako ɗaya bayan da wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta tsaida fara cirar kuɗin daga asusun gwamnoni a riƙa biyan ‘yan kwangilar.
Su dai waɗannan ‘yan gidoga sun kai gwamnonin jihohi 36 ƙara, inda su ka nemi a biya su kuɗaɗen aikin tuntuɓa da su ka ce sun yi wa gwamnonin jihar, tsakanin 1995 da shekarun 2000, su ka taimaka domin a maida wa jihohin kuɗaɗen biyan bashin Paris Club da aka riƙa ɗibar masu fiye da ƙa’ida.
Sun kuma yi iƙirarin cewa sun yi aikin kwangiloli a jihohi 774 tun a wancan lokacin, amma ba a biya su ba.
Yayin da gwamnoni ke tababar ayyukan ‘yan gidoga, su ma shugabannin ƙananan hukumomin Najeriya sun ce a su ga wani aikin da ‘yan kwangilar su ka ce sun yi ba.
A yanzu da Ministan Shari’a Malami ya haƙikice sai an biya kuɗin, PREMIUM TIMES HAUSA ta sake bijiro masu da wannan kwatagwangwa kamar haka:
Hukuncin Da Malami Zai Yi Fatali Da Shi:
Kotu Ta Hana Kwasar Dala Miliyan 418 Daga Kuɗaɗen Gwamnoni A Biya Dillalan Gada-gada:
A ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan gada-gada masu iƙirarin cewa sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi ayyukan adadin kuɗaɗen a shekarun baya.
Dillalan gada-gadar sun ce sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi aikin tuntuɓa ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ƙoƙarin aikin dawo masu da kuɗaɗen da aka riƙa ɗibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.
Babban Mai Shari’a Iyang Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar kuɗaɗen da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.
Gwamnonin 36 sun shigar da ƙarar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, waɗanda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).
A ƙarar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa waɗancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.
Lauyoyin sun ce masu iƙirarin sai an biya su haƙƙin kuɗaɗen har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.
“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi kuɗaɗe a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”
Daga cikin waɗanda gwamnoni 36 su ka kai ƙara, har da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Kuɗaɗen Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.
Discussion about this post