Ba kamar yadda wasu rahotanni su ka ce an kashe sojojin a ranar Juma’a, 22 Ga Yuli ba, gaskiyar magana an yi wannan gumurzun yaƙi a ranar Lahadi, 24 Ga Yuli, da jijjifin safiya.
Makonni biyu kafin farmaki da kuma yaƙin, Makarantar Koyon Aikin Shari’a ta Bwari (Law School, Bwari), Abuja, ta samu wasiƙar gargaɗin cewa ‘yan ta’adda na shirin kai mata hari.
Nan da nan sai makarantar ta sanar wa Bataliyar Sojoji ta 7, wadda Bataliyar Sojoji ce masu gadin Shugaban Ƙasa. Haka wani jami’in soja da ya san komai ya shaida wa PREMIUM TIMES.
“Ai kuwa nan da nan sai mu ka fara sintirin gadin makarantar, inda sojoji 20 tare da motar yaƙi ɗauke da babbar bindigar nan tashi-gari-barde ke kewaye da makarantar a kowane lokaci.
“Akan canja sojojin da wasu guda 20 a kullum. Wannan sintiri da mu ka riƙa yi ya hana ‘yan ta’adda kai wa makarantar hari. Ba don haka ba da tuni sun afka wa makarantar. Amma sai su ka yi kwanton ɓauna a cikin daji, su ka ƙi fitowa.
“Sai mu ka yi tunanin cewa ‘yan ta’addar nan fa ba su rasa tunanin kai hari wani wuri idan ba su samu nasarar kai wa makarantar Bwari ɗin ba. Sai mu ka yi tunanin za su iya kai hari a Jami’ar Veritas, wadda ke kilomita uku da ɗan wani abu daga ‘Law School’. Saboda haka a can ma sai muka riƙa yin sintirin gadin dirshan, kamar yadda aka riƙa yi wa makarantar da su ka so su kai wa farmaki.” Inji jami’in sojan da ya bai wa PREMIUM TIMES wannan labari.
“To daga Jami’ar Veritas, sai mu ka ce bari dai mu riƙa kutsawa a cikin daji, saboda a cikin dare mu kan hangi hasken fitilun cocila can cikin daji nesa.
To da sassafe sai mu ka kai wurin da mu ka taras da an yanka awaki kuma an babbake su da kuma wasu alamomin da ke nuna ‘yan ta’adda sun ɗan yada zango a wurin.
“Da alama ‘yan ta’addar sun gudu sun ƙara hausawa cikin daji, ganin yadda sojoji ke ƙara shiga ciki. A haka sojoji su ka ƙara dannawa, duk da dai ba su san takamaimen inda ‘yan ta’addar su ke ba.” Haka majiya ta biyu ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Dama kuma an ƙara tura sojoji daga Bataliya ta 177 da kuma Bataliya ta 102 da ke Nasarawa da Neja, su ka haɗu da Sojojin Bataliya ta 7 a wurin farautar ‘yan ta’addar.
“Mu ka nemi ƙarin motocin yaƙi da kuma sojojin atileri, duk su ka iso. Ana haka sai mu ka kai inda ke da tsaunuka, duwatsu da kuma ruwa, yadda tilas mu ka ajiye motocin yaƙi. Mu ka yi gaba daga mu sai bindigogi AK47, ko tashi-gari-barde (RPGs) ba mu ɗauka ba. A tunanin mu, ‘yan ta’addar ba su ma kai 30 ba. To ashe sun gan mu, mu kuma ba mu gan su ba. Sai su ka yi mana kwanton ɓauna, su ka riƙa antayo mana gurneti da harbo mana muggan makamai.”
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran Sojoji, Manjo Janar Jimmy Akpor, amma bai ce komai ba.
Yayin da ‘yan ta’adda su ka kashe sojoji takwas, cikin su har da Kaftin da Laftanar, majiyar sojojin biyu duk sun tabbatar da cewa su ma sun kashe ‘yan ta’adda 10.
Bayan kwanaki, sojoji sun sake yin tattaki ciki dajin sun ragargaji ‘yan ta’adda har su ka kashe 30 a yankin dajin Bwari.
Idan za a tuna, kwana kaɗan kuma baya ‘yan ta’adda sun yi bata-kashi da Sojojin Bataliya ta 102 waɗanda su ka kafa shingen bincike kan titin Abuja zuwa Kaduna, a daidai shingen binciken na su.
Gumurzun Bwari ya zo ne makonni uku bayan farmakin da ‘yan ta’adda su ka kai wa Kurkukun Abuja da ke Kuje, kuma kwanaki kaɗan bayan ‘yan ta’adda sun yi barazanar sace Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasiru El-Rufai na Kaduna.
Kafin nan kuma idan ba a manta ba, an kai wa tawagar hadiman Buhari hari, a dajin Dutsinma cikin Jihar Katsina.
Discussion about this post